Siyasa: Dan Takarar gwamna na NNPP a Kano Abba Kabir Yusuf ya Maka Shugaban APC na Jiharsa a Kotu Bisa Kalaman Tunziri

Siyasa: Dan Takarar gwamna na NNPP a Kano Abba Kabir Yusuf ya Maka Shugaban APC na Jiharsa a Kotu Bisa Kalaman Tunziri

 



Dan takarar gwamna na jam’iyyar adawa ta New Nigeria Peoples Party, Abba Kabir Yusuf, Wanda Ake wa lakabi da Abba gida-gida ya maka shugaban jam’iyyar APC mai mulki na Kano,  Abdullahi Abbas, a kotu, bisa zarginsa da kalaman tunziri da É“atanci, karar mai lamba FHC/KN/CS/02/2023 da lauyansa Bashir Tudunwuzirchi ya shigar, ya bukaci babbar kotun da ta gaggauta tilasta wa kwamishinan yan sandan jihar Kano da ya binciki shugaban jam’iyyar APC tare da gurfanar da shi a gaban kuliya a bisa "kalaman da ke haifar da tashin hankali na siyasa a jihar.

Sanarwar mai dauke da sa hannun mai magana da yawun dan takarar, Sanusi DawakinTofa, ta ce dan takarar gwamnan NNPP ya garzaya kotu da nufin tunatar da ‘yan sanda su yi abin da ya kamata, Mun rubuta korafe-korafe da dama tare da Æ™wararan hujjoji kan yawan ta’asar da shugaban jam’iyyar APC na jihar ya yi, amma har yau hukumar yan sanda a Kano ba ta yi wani aiki a kan su ba.

A 'yan kwanakin nan, Abdullahi Abbas, dansa Sani Abdullahi Abbas da wasu makusantansa ne suka shirya tashe-tashen hankula na siyasa da dama, inda aka raunata wasu da ba su ji ba ba su gani ba, aka raunata su da kuma tsoratar da su amma duk da haka, ‘yan sanda sun yi shiru a kan  lamarin duk da rubutaccen korafin da aka gabatar musu.

Ya kara da cewa Idan har kotu ta amince da umarnin, za ta tilastawa rundunar ‘yan sandan Kano su sauke nauyin da kundin tsarin mulkin kasar ya dora mata, tare da yin aiki da irin wannan korafin da aka rubuta a kan shugaban jam’iyyar APC na jihar, Abdullahi Abbas kan zargin kalaman nuna kiyayya, cin zarafi da kuma tallata ‘yan bangar siyasa, zata hukunta shi akan laifinsa

Post a Comment

Previous Post Next Post