Taron wanda ya wakana a yau Alhamis (12 ga Janairu, 2023 ya samu halartar manyar jiga jigan jam'iyyar tare dan takarar shugaban kasa Sen. Rabiu Musa Kwankwaso, PhD, FNSE da mataimakinsa Bishop Isaac Idahosa. A wajen taron, Sen Kwankwaso ya bukaci al’ummar Arewa maso Gabas da ’yan Najeriya da su yi watsi da jam’iyyun APC da PDP da suka gaza,
Sannan su kada kuri’a ga dukkan ‘yan takarar jam’iyyar NNPP tun daga Shugaban kasa zuwa Majalisar Wakilai. Sannan ya mika tutoci ga daukacin ‘yan takarar Gwamnonin jam'iyyar da Sanatoci daga arewa maso gabas a wajen taron.
Taron wanda ya gudana a filin wasa na Tafawa Balewa da ke Bauchi ya samu halartar dimbin magoya bayan jam’iyyar na kasa da shugabannin jam’iyyar na jiha da ‘yan takara.
Tags:
News