IPMAN: Za a ci Gaba da Matsalar ƙarancin man Fetur har nan da Watanni 6 Masu Zuwa

IPMAN: Za a ci Gaba da Matsalar ƙarancin man Fetur har nan da Watanni 6 Masu Zuwa

 



Kungiyar  Independent Petroleum Maketers Association Of Nigeria (IPMAN), ta ce za a ci gaba da fuskantar karancin fetur a fadin kasar har zuwa watan Yunin wannan shekara.  IPMAN takara dacewa, shan wahalar samun mai da ake yi, ya samo asali ne bisa shirin gwamnati na janye tallafin mai baki ɗaya a cikin watan Yuni.

A halin da ake ciki a Nijeriya dai jama’a na fama da matsalar karancin mai tun 2022 har zuwa yanzu musamman a jihohin Arewa, Ba ya ga hakan, akwai tsadar farashin, inda gidajen mai masu zaman kansu ke sayar da man a farashin daban-daban.

banner

A ranar Litinin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, ya ce NNPC na tafka asara kan farashin da ake sayar da man a yanzu. A makon da ya gabata, Ministan Kudi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta ce Gwamnatin Tarayya ta ware Naira tiriliyan 3.6 domin biyan tallafi zuwa Yunin 2023.

Post a Comment

Previous Post Next Post