Gwamnatin Nijeriya Ta Cire Takunkumin Fitar da Itace da Gawayi Zuwa ƙasashen Waje

Gwamnatin Nijeriya Ta Cire Takunkumin Fitar da Itace da Gawayi Zuwa ƙasashen Waje

 



Mohammed Abdullahi, ministan muhalli ne ya bayyana haka a Abuja a ranar Alhamis data gabata bayan wani taron tuntuba da masu ruwa da tsaki a harkar katako da gandun daji su ke yi, Gwamnatin tarayya ta ɗage takunkumin kan  fitar da itace da gawayi zuwa ƙasashen waje amma da “sharadi”.

Read more: Allah Ya Yiwa Fitaccen Ɗan Wasan Barkwanci Maisuna Kamal Aboki Rasuwa

• Batun Canjin Kudi ya Janyo Wahalar Kananan Kudade a Nigeria

Ya ce saka takunkumin ya shafi da dama daga cikin ƴan kasuwa, inda ya ce an dauki matakin ne domin baiwa kamfanoni da masu zaman kansu damar saka hannun jari a harkar noman daji.

Ministan ya yi gargadin cewa gwamnati za ta sanya tsauraran matakai don dakile ɓata dazuzzuka da kuma tabbatar da dorewar kula da gandun daji a kasa baki daya.


           #LABARAI                 #TALLA

Post a Comment

Previous Post Next Post