Taƙaitaccen Sharhi Akan Littafin Tafiya Mabuɗin Ilmi Na Alhaji Abubakar Imam

Taƙaitaccen Sharhi Akan Littafin Tafiya Mabuɗin Ilmi Na Alhaji Abubakar Imam

 



Daga lokaci zuwa lokaci mukan waiwayi litattafan da aka buga a kakar farko ta ƙagaggun labaru da aka rubuta da Hausar boko. Ina nufin ire-irensu Ruwan Bagaja na Alhaji Abubakar Imam; Ganɗoki na Bello Kagara; Shaihu Umar na Abubakar Tafawa Ɓalewa; Jiki Magayi na John Tafida Umaru, da kuma Idon Matambayi na  Muhammadu Sani Gwarzo. Zaka iya ƙarawa da Magana Jari Ce na Alhaji Imam.

Amma akwai wani littafi na Alhaji Imam da zamu iya sanyawa cikin wannan ajin saboda yanda yai tarayya dasu wajen siffofin da suka shigar da waɗancan a cikin litattafan adabin Hausa, ba don yana ƙunshe da ƙagaggun labaru ba ne kamar su. Da ma ina dashi a laburare na, amma ban taɓa karantashi ba. A cikin kwanakin nan na karkaɗeshi, na buɗa, na karanta.

Tafiya Mabuɗin Ilmi littafi ne da mawallafin ya bi wani uslubi wajen rubuta shi wanda ba a saba ba wajen bada irin labarun da littafin ke ƙunshe da su. Ya bi wani salo ne mai ban dariya, mai nishaɗantarwa. A garin karantashi na ƙyalƙyale yafi sau a ƙirga. Kai, har tuntsurewa ma nayi. Kowa ya san cewa Alhaji Imam ba baƙon al’adu da tarihin Turawan Ingilishi ba ne.

Duk da haka, ya zaɓi ya bada labarin tafiyarsa daga Ikko zuwa Ingila ta mahangar wani ƙaton bagidaje. Kai, kace wani littafi ne na zunzurutun barkwanci. Littafin yana ƙunshe ne da irin abubuwan da mai littafin ya gani a halin zuwa da dawowarsa daga Ingila a tsakiyar yaƙin duniya na biyu, da mutanen da ya mu’amalanta a halin tafiya a can Kasar Ingila.

Post a Comment

Previous Post Next Post