Rukunin Farko Na Maniyyata Zai Sauka A Saudiyya Ranar 21 ga Mayu | Hajjin 2023

Rukunin Farko Na Maniyyata Zai Sauka A Saudiyya Ranar 21 ga Mayu | Hajjin 2023



Ma'aikatar aikin hajjin ta bayyana hakan ne yayin wani taron share fage da hukumar Hajji da Umara ta Afirka ta Kudu (SAHUC), Ma'aikatar aikin Hajjin  ta tsara jadawalin jigilar alhazai ta shekarar 2023 zuwa kasar Saudiyya a ranar 1 ga watan Dhul Qa'adah wanda ya yi daidai da 21 ga watan Mayun 2023.

Ma'aikatar ta kuma tabbatar da cewa, ba za a kayyade yawan shekaru ga maniyyatan da ke son zuwa aikin Hajjin shekarar 2023 ba, Sanarwar ta ce an gayyaci hukumar (SAHUC) zuwa kasar Saudiyya nan da mako na 2 ga watan Janairu domin ci gaba da ganawa da ma'aikatar aikin Hajji ta Saudiyya.

Manyan batutuwan manufofin hajjin 2023 kamar yadda SAHUC ta buga su ne kamar haka.

• Babu iyaka ga Mahajjata na 2023

• Za a buÆ™aci rigakafin zazzabin shawara, sanÆ™arau  da takaddun rigakafin covid.

• Ba za a buÆ™aci gwajin cutar korona ba, da dai sauransu.

Post a Comment

Previous Post Next Post