In ba ku manta ba a kwanakin baya gwamnan bankin nigeria Godwin Emefele ya fitar sanarwar sauya fasalin takardun kudin naira, canjin zai faru ne akan naira 1000, 500, zuwa dari 200 kadai.
Kamar yadda shugaban kasa Gen. Muhammadu Buhari yayi bayani cewa wadannan kudaden da za'a canja an basu wa adi na tsahon wata uku, Tun daga watan october na shekarar 2022 zuwa 31, ga watan janairun 2023 mai zuwa.
Wannan yanayi da ake ciki ya janyo karin kai kudade bankuna domin ajiya a sanarwar da bankunan suka fitar, a bangare guda kuma, wannan yanayi ya janyo wahalar kananan kudaden da suka tsallake wannan canji, irinsu naira 100, 50, 20, zuwa naira 10 hardama naira 5.
Asua Daily Post ta shiga kasuwanni inda ta zanta da masu kananan sana'oi daban daban, yan kasuwar sun bayyana yadda suke fama da wahalar kananan canji ka. kamar yadda wani mai sana'ar sai da kayan miya ya shaida mana yadda wahalar canjin ta janyo masa asarar costumer sama da guda 5 a dalilin rashin canjin da ake fama da shi.