Buhari Ya Kaddamar Da Sabbin Takardun Naira Ayau

Buhari Ya Kaddamar Da Sabbin Takardun Naira Ayau

 



A yau Laraba ne dai shugaban ƙasa Gen. Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabbin takardun Naira da aka sake wa fasali. In baku manta ba a watan jiya ne dai babban bankin Nijeriya, CBN, ya sanar da cewa zai sake fasalin Naira 1000, 500 da kuma 200 da ga ranar 15 ga watan Disamba.

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ne ya bayyana haka ga manema labarai a jiya Talata a wajen taron kwamitin tsare-tsaren kuɗi, Emefele ya ce babban bankin ƙasa ba zai sauya ranar ƙarshe da ya saka na mayar da tsoffin kuɗin zuwa bankunan ƙasar domin sauya su da sabbin takardun kuɗin ba.

Ya kara da cewa shugaban zai Æ™addamar da sabbin takardun kuÉ—in a lokacin taron majalisar zartarwa na Æ™asa, Tun a ranar 26 ga watan Oktoba ne dai gwamnan babban bankin Æ™asar ya sanar da cewa  za a ci gaba da kashe sabbin kuÉ—in tare da tsoffin kuÉ—in har zuwa ranar 31 ga watan Janairun 2023, lokacin da za a daina karbar tsoffin Æ™udin.

Post a Comment

Previous Post Next Post