Takaitaccen Tarihin Marigayi Hassan Sarkin Dogaran Kano

Takaitaccen Tarihin Marigayi Hassan Sarkin Dogaran Kano

 



Hassan Adamu, da aka fi sani da Hassan sarkin Dogarai, shine sarkin Dogarai na uku da marigayi sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ya nada a mastayin shugaban dogaran sarki a shekarar 1990, Kafin nadin Hassan a matsayin sarkin dogaran fadar Kano, Marigayi Ado ya nada wasu mutane biyu a baya wadan nan mutane kuwa sune Adamu da Dan Wudil kuma bayan mutuwar Adamu ne aka nada Hassan, sannan shi ma bayan mutuwarsa aka nada sarkin Dogarai na yanzu, Dan bala.

Sai dai sabanin sarkin dogarai Adamu da Dan Wudil, Hassan ba bafade bane. Asalinsa direba ne dake sana'ar tuka mota kafin daga baya ya zama hadimi ga galadiman Kano, Marigayi Tijani Hashim, mutumin da ya fara nada shi a matsayin shamakinsa kuma ya zama silar shigar sa cikin fadar Kano.

A shekarar 1990 ne, bayan mutuwar sarkin Dogarai Dan Wudil, Marigayi Tijani Hashim ya roki sarkin Kano Ado alfarmar ya nada Hassan a matsayin sarkin Dogarai saboda tsananin biyayyar sa da kuma jarumtar sa, sannan ga soyayya da yake nunawa ga sarkin.

Marigayi Hassan na zaune ne da iyalinsa a unguwar Sagagi, kusa da gidan mahaifiyar Ado Bayero, kafin daga bisani ya koma unguwar gidan sarkin Dogarai dake unguwar Dogarai, daf da gidan sarkin Kano. Hassan ya yi shura a cikin sarakunan Dogaran Kano saboda karfi da jarumta da kuma tsananin biyayyarsa ga sarkin Kano Ado.

Hassan sarkacecen mutum ne, saboda girma da tsayinsa har kirari ake yi masa da Bishiya
Marigayi Hassan ya fara haduwa ne da shahararren mawakin Hausa, Alh Dr. Mamman Shata, yayin da yake sana'ar sa ta tuka mota. Bayan Hassan ya zama sarkin Dogarai ne, Shata ya rera masa wakar "Hassan sarkin Dogarai" wakar da ta kara daukaka sunan Hassan a fadin Duniya, Yanzu haka iyalan Hassan sun koma gidansa dake unguwar Sagagi inda suka cigaba da rayuwa bayan rasuwarsa.

Post a Comment

Previous Post Next Post