Ga wasu Abubuwan da ya kamata mutane su sani game da sabuwar Na'urar zaɓe wadda za ayi amfani da ita a zaɓen shekara ta 2023 mai gaba towa in Allah yakaimu
1. Babu maganar over vorting.
2. Babu maganar jiran tsayawa kidayar kuri'u bayan an kammala zabe, saboda kana zabar Jam'iyyar da kake so, na'urar tana recording ɗinta a cikinta, kuma take zata tura kuri'un wurin tattara sakamakon za6e na jiha da na Ƙasa.
3. Babu maganar tsayawa tantance masu jifa kuri'a. Da kazo za'a dauki hotonka da computar domin a tabbatar da kaine mai wannan katin zaben, daga nan sai na'urar ta baka damar yin zaben. Saboda haka ba za'a dauki lokaci wurin jifa kuri'a ba, Dan haka za'a kammala zabe cikin lokaci ba sai an kai dare ba.
4. Babu maganar amfani da Balot paper wurin jifa kuri'a, saboda akwai alamar kowacce Jam'iyyar wanda mutum yake so a cikin wannan na'ura. ka na zaben Jam'iyyar da kake so, zata fitar da slip ko kuma ince Ballot paper nata na kanta, kuma ta saka shi cikin akwatinta da kanta.
5. Babu maganar invalid a wannan za6en na 2023. Saboda duk alamomin jam'iyun Najeriya suna a cikin wannan na'ura, idan ma baka iya amfani da ita ba za'a gwadama yanda zaka za6i jam'iyar da kake so.
6. Babu maganar yin za6e sau biyu ma'ana kayi zabe ka dawo ka kuma yi saboda da zaran wannan na'ura tayi maka hoto kuma kayi tumbprint, to babu yanda zakayi kayi ka kara yin zabe sau biyu, koda kuwa ka koma wata rumfar zaɓen ne. Saboda kana zuwa daga anyi ma hoto kuma kayi tumbprint na'urar zata fidda bayananka cewa kayi zabe a wata rumfa kuma bazata taba baka dama kayi wani ba, saidai kayi hakuri.
7. ya kamata a sani wannan Na'ura babu yadda za'ayi wani yayi za6e da kuriar wani, saboda kana kara katinka a jikin na'ura, za ta daukeka hoto, kuma zata yi searchig dan ta gano idan katin nakane ko ba naka bane. Idan naka ne sai tabaka dama kayi zaɓe, idan ba naka bane bazata baka damar yin zabe da shi ba.