Tarihin Sana'ar Kadin Auduga a Kasar Hausa

Tarihin Sana'ar Kadin Auduga a Kasar Hausa

 



Asalin Kadi kakanninmu wanda karfinsu ya kare a da ba su zaman banza, za ka ga sune ke kadi, su na mai da wannan auduga zare da mu ke dinki da shi, Duk da a na ganinsu karfinsu ya kare kuma a na ganin kamar ba komai suke iyawa ba ga wanda bai san sirrin lamarin ba, amma idan tsohuwa ta daga taskirar kadinta sai taiwa jikanta aure ko kuma ta sai ma sa gona ko ta gina masa gida.

Kuma abin alfahari ga wannan sana'a bata tara wasu karikicen kayan aiki, mazari dai shine jigon aiki wanda ake kadawa, sai Alli wanda ake shafa wajen ana taba Auduga ana nadawa mazari audugar tana komawa zare. Sai Taskira wacce ake ajiye komai da ake bukata na aikin kudi a cikinta.

A yanzu ma duk da zamani ya canza, sana'ar kadi mu na ne ma mu yi watsi da ita, to duk da haka akwai canjinta, ga wanda ba sa son motsa jikinsu akwai saka da ake yi da wasu yan tsinkaye da ake kira kwarashi, Sai dai wannan zuwan nasara muka same su da kuma zaran da ake sakar da shi wanda shi ma amurje ake samun su, wanda ake kira Ulu. Irin wannan sakar har riga ana sakawa zuwa su wando, da hula amma mutanan namu sun fi mai da kai wajen yin kayan yara.

Post a Comment

Previous Post Next Post