Tarihin Asalin Sana'ar Farauta Da Yadda Ake Yinta | Mafarauta

Tarihin Asalin Sana'ar Farauta Da Yadda Ake Yinta | Mafarauta

 



A da kafin ci gaba ya zo wa dan Adam, ba shi da wata sana'a wadda ta wuce farauta, farauta ce ka dai hanyar da suke bi suke rayuwa, don lokatai masu nisa da suka shude ko hikimar noma dan Adam ba shi da ita sai farauta kawai ya sa a gaba, daga baya da ci gaba yazo jama'a su ka bazu.

Ita dai farauta a zamani mai tsaho da ya shude dole ce take sawa ayi ta don babu wani abin yi, amma daga baya wasu sana'o'i da suka samu sai ya zama masu sha'awa suke yi, bayan sha'awa, da taurin zuciya da rashin tsoro da kuma shiri sosai.

Read more: Sirrin Sana'ar Kira a Kasar Hausa | Makera

• Takaitaccen Bayani Akan Sana'ar Su | Kamun Kifi

A bangaren hausawa kuwa Farauta wata Al'ada ce ta mallam Bahaushe wacce akanyi lokaci bayan lokaci Duk da akwai wadanda suka dauki farauta a matsayin Sana'a har sukan yi tafiya zuwa wani gari kuma sukan kwana a daji kuma abincin su kacokan ya dogara ne akan namun daji da kuma 'Ya'yan itatuwa a lokacin da suke cikin Daji Amma mafi akasari ana shirya Farauta ne tsakanin garuruwa da yawa, Kusan duk shekara akan shirya farauta a hadu domin shiga daji yin farauta.

Farauta ba kowa zai iya ba, don ga wanda bai san farauta ba a ka ja shi sai ya ga kamar halaka shi za'a yi don abin ya zama kamar sai da rai yadda mafarauci yake shiga daji yana haduwa da manyan dabbobi da kwari masu hallaka mutum lokaci guda, amma haka wasu za su kwana a cikin wannan hadari, kuma har ta kai su da samun dama su kama kananan dabbobi su dawo in sun dace har manyan dabbobi su kan kai kasa.

Amma mafi yawancin masu farauta wanda su kan yi suna su shahara bada ka su kanyi ba su kan nemi magunguna na tsaron kai daga irin hadarurrukan da suke shiga. Ka san wani lokaci mai shiga daji kamar mai shiga ruwa ne, da ka sukan shiga tun da basu san mai za su taras ba, yadda mutane ke farautar dabbobi haka suma mutanen nan dabbobi ke farautar su.

Post a Comment

Previous Post Next Post