Tarihin Asalin Ginin Gidan Sarki Na Jihar Kano Wanda Ake wa Lakabi Da Gidan Rumfa | Gidan Dabo

Tarihin Asalin Ginin Gidan Sarki Na Jihar Kano Wanda Ake wa Lakabi Da Gidan Rumfa | Gidan Dabo

 



Wannan gida ya dade, Asalinsa wani sarki ne ya gina shi wannan Sarki ana cewa da shi Sarki Muhammadu Rumfa. Dalilin ma da har yanzu akewa wannan gida lakabi da Gidan Rumfa kenan Rumfa ya gina wanan gida ne a shekarar 1479 miladiyya.

Ance Sarkin gininsa mai suna (Danjigawa) shine ya yi wannan gini, ya shekara uku yana yin ginin. Sarki Rumfa ne yasa akayi kofofi guda uku, wadannan kofofin sune Kofar Kudu, Kofar Arewa (Fatawa) da kuma Kofar Yamma wadda ake cewa kofar Kwaru.

Kuma yawancin gine-ginen farko sune har yanzu Amma inda kofofin shiga da sorayen su suke an sami gyare-gyare da yawa a zamanin Sarki Abdullahi Bayero don shi mutum ne mai son yin gine-gine, wani lokacin da kansa yake tsara gini Ya fasalta shi, kai har awani lokacin a gina da shi.

ALSO READ: Takaitaccen Tarihin  Makarantar Gidan Makama | Makama Special Primary School kano

• Tarihin Masarautar Kano Daga Mulkin Maguzawa Zuwa Fulani

• Takaitaccen Tarihin Sarki Alhaji Abdullahi Bayero

Sannan duk sa'adda ya yi tafiya idan ya gano wani sabon fasali sai ya dawo ya fasaltawa maginansa Su gina, A da duk yawancin dakunan gidan na jinka ne a hankali sarki ya maida su soraye.

An kasa gidan Sarki zuwa kashi uku a tsaye wato daga kudu zuwa Arewa,  shi cikin gidan wajen da unguwanni suke shi ne a tsakiya, sannan ta gaban kofar kudu akwai wasu manya-manyan filaye daya a gabas daya a yamman gidan.

Wadannan filaye ana kiransu da sheka, Ana cewa Shekar Gabas da Shekar Yamma. A cikin gidan anyi unguwanni da dama. An tsara gidan kamar wani dan karamin birni, Unguwannin da da suke cikin gida suna da yawa, wadannan unguwanni sun hada da Yalwa, Dutse Babba, Sokoto, Kacako, Unguwar Bare-bari Unguwa uku, Garko farin gida, Sabon Soro, dogon gida da soro wato soron sarki Da kuma soron mallam Dabo.

Wannan soro na mallam Dabo, Mallam Dabo ne Sarki na biyu a jerin sarakunan kano ya fara zama a wurin kuma dukkan sarkin da zai shigo gidan ba  zai fara zama a ko ina ba sai ya dangane da dakin shekara da yake a Kacako sa'annan ya taho soron mallam ya kwana uku kafin ya shiga soron sarki, Su kuwa matan Sarki ko wacce tana da wajenta Daban.

Post a Comment

Previous Post Next Post