Adinin gargajiya wata hanya ce ta bautar da mutane dabam-daban kan sama wa kansu. Babu wata kabila da za ta bugi kirji cewa ita ta koya wa wata bauta wa (Ubangiji). Kusan kowace kabila nan take take ta kago hanyoyin bautarta. Wadannan hanyoyin bauta ana ganin sun samu tun farkon samuwar dan’adam. Masu binciken tarihi na ganin cewa makasudin bautar gumaka shi ne ganin cewa wasu abubuwa kamar rana da wata da kogi ko duwatsu suna yi dabi’a irin ta mutum wato in an faranta musu rai su ji dadi in kuma an bakanta musu su yi fushi.
Masu bauta wa kogi ana ganin sun yi imani da shi ne saboda ganin cewa wani lokaci sai ya yi ambaliya su sami amfani mai yawa, wani lokaci kuma ya bushe. Daga ya bushe sai masu bautar su dauka cewa sun yi wani laifi ne, sai a sami wani babbansu ya kasance mai yin magana da gunkin, shi kuma zai rika gaya musu sakon gunki. Makasudi na biyu da ake zaton ya sa mutane yin bautar gunki shi ne ta wajen ciwo.
Wani lokaci ciwo kan kama mutum a yi ta magani a rasa yadda za a yi ciwon ya warke. To, in aka yi katari wani ya zo ya ba da magani majinyacin ya warke, sai a dauka cewa wannan mutumin yana da wata daraja ta musamman. Saboda haka duk abin da ya faru, shi za a dosa, shi kuma ya rika dangana cuce-cucen da iskoki. Ta nan ne sai mutane su yi imani da iskoki.
Tun da yake za a yi magana ne a kan addinin gargajiya na Bahaushe, ya kamata a dan bayyana wasu misalai na tsafe-tsafen Hausawa a lokacin da suke yin Maguzanci da kuma barbashin tsafe-tsafen har zuwa yau. Amma tun da ba Bahaushe ne kadai yake yin irin wadannan tsafe-tsafe ba, za a bayar da takaitaccen misalin bautar gumaka a wasu kasashen.
Misali a kasar Masar suna da nasu gumakan kafin zuwan musulinci, sanannu daga cikin gumakan su ne Ra da Osiris. Ra shi ne gunkin rana shi kuma Osiris shi ne mai kula da kogin Nil, kogin da shi ne kashin bayan rayuwar mutanen Masar. Idan muka matso wajen makwabtanmu za mu ga cewa Ashanti na kasar Ghana su ma suna da sanannen gunkin da suke kira Abosomi. Yarabawa kuma suna da Orisha.
Orisha din nan shahararren gunki ne wanda Yarabawa ke wa bauta sosai. A duk lokacin da suka ga wani abu ba ya tafiya daidai, sai manyansu su kai kukansu ga wannan gunki. Daga nan sai a yi yanke-yanken dabbobi don Orisha ya sha jini. Da an ga wani canji sai a dauka cewa Orisha ya yarda. Mutanen Jukun ma suna da nasu gunkin da suke kira Jo. Barebari kuma na da nasu gunkin da suke kira Sanama. Kabilar Tangale da ke Bauchi ma ba a bar su a baya ba wajen bautar gumaka, suna da babban gunkinsu da suke kira Yeku. Ban da babban gunki Yeku akwai kuma kananan gumaka a kowane gida da ake bautawa, haka kuma a kowace unguwa.
Daga wadannan bayanai da aka yi za a fahimci cewa addnin gargajiya ya mamaye kasashe da yawa kafin zuwan addinin Almasihu da na musulunci. Kuma kusan kowane irin addinin gargajiya, sai an sami wani mutum wanda shi ne mai wucewa gaba don nemo bayani daga gunkin sa’annan ya sanar wa da mabiya.
Tun da yake an dan ji bayanan addinan gargaji na wasu mutane, sai kuma mu tsunduma ga na Hausawa. Hausawa ma kamar sauran mutane suna da addininsu na gargajiya tun kafin zuwan addinin musulunci. A gaskiya ba wanda zai ce ga lokacin da Hausawa suka fara bautar gumaka da tsafe-tsafe. Tarihi ya nuna cewa tun da aka halicci dan’adam, bautar iskoki ta cusu a zuciyarsa. Wannan shi ya sa yake da wuya a bayyana tun sa’ad da abin ya fara.
Dalilai na biyu da ake jin su suka haifar da addinin gargajiya, ba kuma ga Hausawa kadai ba har ma da sauran jinsi iri-iri na duniya. Dalili na farko shi ne, shi dai dan’adam ya dauka cewa kowane abu a duniya yana dabi’a irin tasa, wato wani lokaci zai ji dadi musamman in an faranta masa rai, ya kuma ji zafi in an bakanta masa, har ya kai ga ramuwar gayya. Alal misali.
lokacin da Kanawa ke bautar Tsumburbura a gindin Dala, zamanin Barbushe, duk shekarar da ta zo da wani bala’i sai mutane su dauka cewa lallai an sabawa Tsumburbura. Saboda haka sai a yi yanke-yanken awaki da karnuka don dodon ya sha jini wai ko ya huce. To wasu lokutan kuwa sai a yi sa’a abin ya yi sauki shi ke nan sai a dauka wannan sauki ya faru ne saboda yanke-yanken da aka yi wa gunkin ne.
Dalili na biyu da ake zaton shi ma ya taimaka wajen kago bautar gumaka shi ne ciwo. Sau da yawa akan sami ciwo ya ki ci ya ki cinyewa ga mutum, a yi ta neman magani, amma a banza, sai a dauka ba mai warkar da majinyacin sai dai mutumin da Allah ya yi wa wata daraja ta musamman. Ana nan har a sami wani boka ya nuna cewa iska kaza ce ta taba mutum amma shi zai warkar da shi. Idan aka yi katari sai kuwa mutumin ya warke. Da zarar haka ta faru fa sai mutane su yi imani da wannan iska da boka ya ambata, shi kuma boka kasuwa ta bude ke nan.
Ana yin bauta ta hanyoyi dabam-daban. Wasu sukan sassaka gunkinsu da kansu, su yi wani mutum-mutumi su rika bauta masa. Wasu kuma sukan bauta wa iskokai, Dangane da bautar gumaka wajen Hausawa, su ba sa sassaka gunki don yi masa bauta, a’a, sai dai bautar iskokai ta hanyar bori. Kanawa suna bautar Tsumburbura a dutsen Dala.
Akwai wasu gumaka makamantan wadannan a wasu wurarae a kasar Hausa. A kasar Katsina, akwai mutanen Kainafara, arnan Birci a kasar Dutsin ma, masu bautar wani gunki mai suna Dan talle. Sunan mai kula da wannan gunki shi ne Sarkin Noma. Kamar Barbushe Sarkin Noma shi ne mai ba da labarin sakon da Dan talle ya yi ga mabiyansa. Su ma mabiyan Dan talle kabilar Kainafara na yin bikinsu ne shekara-shekara kuma suna yin yanke-yake kamar dai mutanen Barbushe.
Akwai kuma wasu maguzawa masu bautar wani gunki mai suna Magiro a dutsen Kwatarkwashi a cikin jihar Sakkwato. Mai kula da tsafin shi ne Magajin Ranau. Shi ma ana yi masa yanke-yanke kamar yadda ake yi wa Tsumburbura sai dai su bakin sa ake yanka masa ko bakar akuya, Bayan wadannan gumaka kuma, Hausawa Maguzawa kan yi tsafe-tsafe na gida. Misali shi ne, kusan kowane Bamaguje ya ajiye wata halitta wadda ya dauka ita ce kan gidansa. Wasu sukan dauki dabbobi kamar damisa, kura ko zomo ya zama kan gidansu. Duk abin da aka dauka ya zama kan gida to ba hali wani dan gidan ya ci namansa, ko ya kashe shi ko kuma ya cuce shi ko ta wace hanya.