Tarihi ya nuna cewar an gina kofar Marusa ne a wajen karni na 15, an ginata ne a daidai lokacin da aka gina sauran ganuwowin Katsina saboda masu kawo hare-hare a Zananin da ake yake-yake a tsakanin Garuruwan da Sarakuna ke Mulki domin a kara Fadada kasar Mulki.
Bincike ya nuna cewar kofar ta samu sunanta ne daga wani Basarake na Habe da yke mulkin Dutsi, mai suna Marusa Usman, Ta wannan kofar ce Marusa Usman din ke bi in zai tafi inda ya ke sarauta wato garin Dutsi da ke Gabashin birnin Katsina, kuma tanan yake shigowa.
Daga nan ne aka sanya ma ta sunan Basaraken ta zama kofar Marusa, Bincike ya Tabbatar da cewar ya zuwa yanzu Kofar Marusa ta kai fiye da Shekaru Dari 500 da kafuwa a inda ta ke sannan Wasu masanan tarihi suna cewa an Dade ana son a Rushe kofar Amma ba a yi Nasara ba saboda Tsatsube-tsatsube da Surkullen da aka yi a lokacin da aka Gina kofar a shekaru Aru-aru da su ka gabata.