Daura na daya daga cikin manya manyan kasashen Hausa, A lokacin Tana da mata a matsayin Sarauniya, Wadanda suke mulki a wancan lokaci, A lokacin Sarauniya Daurama, akwai wata rijiya mai suna Kusugu, wadda itace babbar rijiya dake ba garin Daura ruwa a wancan lokacin. Amma mutane basu samun damar dibar ruwan sai ranar juma'a-juma'a saboda akwai wata Macijiya a cikin rijiyar.
• Tarihin Asalin Ginin Gidan Sarki Na Jihar Kano Wanda Ake wa Lakabi Da Gidan Rumfa | Gidan Dabo
• Tarihin Masarautar Kano Daga Mulkin Maguzawa Zuwa Fulani
• Takaitaccen Tarihin Sarki Alhaji Abdullahi Bayero
Haka mutanen garin suka cigaba da zama har saida wata rana wani mutum wanda ake tsammanin Dan Sarkin Bagadaza ne, Abu Yazid ya zo Daura bayan da ya kasa samun Sarki bayan mutuwar baban shi. Jarumin Dan Sarkin bayan daya sauka gidan wata tsohuwa mai suna Ayyana, sai ya bukaci a bashi ruwa ya sha. Ruwan da aka bashi bai ishe shi ba, shi da mutanen shi. Sai ya roki tsohuwar data nuna mashi inda rijiyar garin take domin ya debo ruwan. Tsohuwar sai ta gargade shi akan Macijiyar amma bai ji ba. Bayan da yaje debo ruwan sai sukayi artabu da Macijiyar inda ya kashe ta tahanyar sare mata kai da takobin sa kamar yadda tarihi ya nuna.
Ganin irin jarumtar sa haka ya sanya Sarauniyar ta aure shi inda ya zama Sarki. Saboda baya jin Hausa hakan ne ya sanya mutane ke ce mashi Bayajidda. Watau, Bayajjida. Ya haifi yara bakwai wadanda sune sukayi mulkin kasashen Hausa guda bakwai, Ƙasashen Hausa bakwan dai sun haɗa da Daura da Kano da Katsina da Zazzau da Gobir da Rano da kuma Biram ko kuma Haɗeja.