An haifi Dr. Yusuf Maitama Sule a Shekarar 1929, a unguwar Yola, cikin garin Kano. Maitama shine na uku a jerin 'ya'yan gidansu, Rabi, wacce ake kira Yaya ta Zage, Maimuna wacce ake kira Yaya ta Bichi. Ansa masa suna Yusuf, saboda sunan Mahaifin Madakin Kano Mahmudu, shi Madaki yana kiranshi Abbana. Sunan Maitama kuwa ansa masa shine saboda Galadiman Kano Yusuf, saboda anyi amfani da makamai sosai lokacin basasar Kano.
Akan yiwa duk wani mai suna Yusuf lakabin Maitama. Madakin Kano yayiwa Mahaifin Maitama, Abba Sule Danmuri, mukamin mai kula da dukkan al'amuransa na gida da kula da Dawakai. Maitama, yana dan shekaru hudu mahaifiyarsa Hauwa, wacce ake kira 'Yarkayi ta rasu. Ita Allah yayita ne mace mai ban dariya, mai raha, bata fushi, shi yasa duk bukin da ya tashi ita ake kira tayi ta magana a gidan buki, halinta da iya maganarta Maitama ya gado.
Read more: Takaitaccen Tarihin Sarki Alhaji Abdullahi Bayero
• buwan Cigaba Da Gwamna Rimi Yayiwa Kano A Zamaninsa
• MULKIN SOJA: Hawan Birgediya Murtala Ramat Mohammad Shugaban Kasa
Madakin Kano ya saka Maitama a makarantar Elementary ta Shahuci a cikin watan Janairu, 1937, dama kafin akaisu makarantar boko, suna yin karatun kur'ani a gida. A ka'ida shekaru hudu ya kamata ayi a elementary, amma saboda hazakar da Maitama ya nuna shekaru biyu kawai, yayi aka bashi damar yin jarabawar zuwa gaba.
A wannan lokacin ne Maitama ya fuskanci kalubalen da bai taba fuskanta ba a rayuwarsa. Domin a wannan gabar ne Madaki Mahmudu, mai daukar dawainiyarsa a rayuwa ya rasu cikin shekarar 1939. Aka bar kujerar Madaki, tsawon shekaru biyu, ba'a nada kowa ba, har sai a shekarar 1941.
Gaba daya dawainiyyar Maitama ta koma kan Mahaifinsa Abba Sule, wanda a wancan lokacin bashi da karfi. A shekarar 1943 Maitama ya shiga kwalejin Kaduna, yana dan shekaru 13. Maitama, ya kammala karatunsa na kwaleji cikin shekarar 1948, ya kuma kama aikin Malanta, a makarantar Middle ta Kano.
Maitama sun tsaya zabe dashi da tsohon Malaminsa a makaranta, Malam Aminu Kano, wannan zabe ya gudane a Central Office, Alhaji Yusuf Maitama Sule, ÆŠanmasanin Kano, malamin makaranta ne, kuma É—an siyasa sannan kuma basarake. Tabbas, Alhaji Yusuf Maimata Sule, ÆŠan masanin Kano, ya bayar da gagarumar
gudunmawa wajen ciyar da É—aiÉ—aikun mutane gaba har zuwa kan gwamnatin tarayya.
Da shi aka yi fafutikar Æ™watar ‘yanci da kuma ganin yunÆ™urin tabbatar da haÉ—in kan Æ™asa da É—orewar zamanta a matsayin Æ™asa guda. Alhaji Yusuf Maitama Sule, ÆŠan masanin Kano, ya yi aiki da sarakunan Kano biyar, da kuma gwamnan Kano Audu BaÆ™o, sannan kuma ya yi aiki da shugabannin Najeriya tun daga kan Dr. Nmandi Azikwe, har zuwa hawan shugaba Buhari na biyu
(2017).
Wasu lokutan kai tsaye ta hanyar riƙe wani muƙami a cikin gwamnati, wasu lokutan kuma a bayan fage kamar yadda ta faru a zamanin Janar Muhammadu Sani Abacha, Haka nan kuma a dimokuraɗiyyance, da shi aka kafa jamhuriyyar farko, ta biyu, ta uku, da ta huɗu da mu ke ciki a yanzu. Yana da ƙwarewa a fannin siyasa ta gida da kuma wajen Najeriya. Allah ya karbi rayuwar yusuf maitama sule a ranar litinin 3th July 2017 miladiyya wanda yayi dai-dai da 9 ga shawwal 1438 hijiriyya.