Ta'addancin Da Ƙasar Ingila Tayiwa Indiyawa a Zamanin Mulkin Mallaka

Ta'addancin Da Ƙasar Ingila Tayiwa Indiyawa a Zamanin Mulkin Mallaka

 



A Shekarar 1876 zuwa 1879, karkashin mulkin mallaka na ƙasar Ingila da ta yiwa Indiya, an yi wani baƙin fari mai ban mamaki, wanda yayi sanadiyar rasuwar mutane sama da Miliyan Goma da ɗoriya. Wannan baƙar yunwa wadda ta yi tsanani a kudancin ƙasar, ta yi sanadiyar rushewar ƙauyuka, Dangi, da kuma sa mutane su kashe kan su saboda yunwa.

Ƙasar Ingila ta yi halin ko in kula da halin da mutane ke ciki, inda suka kalli ma lamarin a matsayin hanyar da "Nature" ke bi wajen dai-daita ƙididdigar haihuwa, da kuma rage adadin mutane a duniya, inda su ka yi amfani da Nazariyar Thomas R Malthus, wadda ke ƙunshe da hakan.

A gefe guda kuma suka cigaba da amfani da dokar " forced export" wato dokar da ta sahale musu ɗebe abincin indiyawa zuwa ƙasar su ba tare da sun ji tausayin wannan halin da waɗanda suka noma abincin ke ciki ba, har ta kai da yawan manoma na kashe kan su dan kar iyalan su su rasa abincin ci saboda rayuwar su. Galibin waɗanda wannan bala'i ya kashe sun kasance mata da ƙananan yara.

Idan kun lura da kyau, za ku ga a cikin shekaru biyar bayan nan, Manya-manyan kamfanonin finafinan indiya, sun matsa da yin Films da ke nuna yadda Ingila ta zalunce su, ta kuma ɗebe arzikin kasar zuwa ta su, a matsayin hanyar ɗaukar fansar rashin imanin da aka yi musu, da kuma fallasa asirin Ingila da Turawa akan ta'addancin da su ka yiwa Duniya da sunan mulkin mallaka.

Ga sunayen Finafinan da suke nuna bakin zaluncin da ingilawa sukayi musu.

• Thugs of Hindostan 2018.
• Shamshera 2022.
• Sye Raa Narasimha Reddy 2019.
• RRR 2022.

Post a Comment

Previous Post Next Post