Sirrin Sana'ar Kira a Kasar Hausa | Makera

Sirrin Sana'ar Kira a Kasar Hausa | Makera

 



Kira sana'ar mu ce da muka ginu akan ta shekaru aru-aru da suka shude wannan sana'ar alherin da yake cikin ta Allah yayi yawa da shi Da wuya mai yin Wannan sana'a ya yi kukan babu domin sana'a ce da ta bada zabi da yawa  kuma wannan sana'a sinadari ce ta sauran sana'o'i don haka mai yin sana'ar kira da wuya yayi kukan wani kaya na su yayı nauyi ko kuma babu aikin yi na dan lokaci

ALSO READ: sana'ar Jima a Kasar Hausa | Majema

• Tarihin Sana'ar Kadin Auduga a Kasar Hausa

Don mai yin kira kusan koda yaushe cikin zafin wuta yake Komai zafi kuma  Komai sanyi, don wutar ce abokiyar aikinsa. makeri yake amfani da zuga-zugi wanda ya ke hura wuta da shi kuma wutar da Makern yake amfani da ita, ta gawayice, don ba sa amfani da itace wannan wuta da makeri yake hurawa, ita ya ke sa karfe a ciki in yayi ja sai ya dauko shi da Hantsakı, wasu kan kirashi da araflaki.

Yayin da Makeri ya dauko karfen ya kan dora akan uwar makera  wannan wani karfe ne da suke shinfida suna dora karfen daza'a sarrafa bayan an dora karfen  akan uwar makera, su kan daki karfen da asaba, har sai ya yi fadi, yayin da yayi fadi sosai, sai su sa mantalaga su gyara surar abin da ake nufi, ko menene.
     
Dama ance makera suna da zabi wasunsu su Kan yi amfani da bakin karfe, sune wanda aikin su yafi yawa da 'yar wuya, don karfen yafi kwari, su Kan kera bakaken abubuwa kamar manyan kofofin irin na da, zuwa makamai da kayan noma da sauransu,  masu aiki da farin karfe su ne yawanci su kan yi kayan da ake cewa gorar ruwa ko kumfar karfe.

Post a Comment

Previous Post Next Post