Muhimmancin Sana'ar Noma | Asua Daily Post

Muhimmancin Sana'ar Noma | Asua Daily Post

 



Noma tushen arziki, noma jigon rayuwa, noma tushen ciniki sana'ar noma itace sana'ar da tafi kowacce sana'a mahimmanci, domin rayuwa ba za ta yiwu ba sai da abinci, mafi yawancin sana'o'i baza su samu ba sai da noma, dabbobi in babu abinci ba za su rayuba, babu maganar kiwo da jima, haka ma dukanci, zuwa fawa duk inda aka leka sai a ga noma ya hada wurin.

Idan muka waiwayi noma sai muga babu abinda da ya kamata muyi sai godiya ga Ubangiji da Ya bamu ni'ima, domin albarkar noma wata rahama ce da Ubangiji Ya yi mana ba wata dabarar mu bace ko hikima, don ba wani abu mu ke ba sai illa dan irin da muke tanada idan Allah ya bamu ruwa muyi shuka, sai dan noman da zamu yi, zuwa yar huda da zamu yi har Allah Ya albarkaci abinda muka shuka, mu sami amfani mai yawan gaske.

ALSO READ: Yadda Ake Noman Shinkafa a Zamanance Kashi Na Biyu

• Yadda Ake Kiwon Kifi A Zamanan ce - Asua Daily Post

Babu ciniki mai ribar noma don sai mun shuka iri, kamar na wake ko dawa, bai kai ya kawo ba kaga mun tashi da buhunhuna, hatta kai mu da bada zakka. A daure a yi noma shine yafi komai muhimmanci da riba, a noman kuma wani karin albarka da Allah yayi mana har da rani a kan yi noma yanzu, wannan dama ce ga mutane da suke da dan gulbi ko kogi da dam a kusa da su, irin ma su noman ranin nan idan abin ya karbesu, har sun fi masu yi da damina, koda yake noma duk noma ne, albarkar ake nema cikinta.

A yanzu da yake an sami ci gaba har da shanu akanyi huda maimakon mutum yai ta fama in yana da hali sai ya sai shanu su taimaka masa in kuma bashi da su sai ya bawa mokwabcinsa lada ya taimakamasa da su, ban da shanu yanzu har da mota mai yin huda a wasu bangarori banda huda, ance inda suke ci gaba har da mota mai yin girbi ta yi chasa.

Amma mu abin alfahari a gare mu babu motar ba shanun da haka muka yi arziki da noma. babu wani abu mai wuya sai illa bawa abin muhimmanci da kula da yin noman da zuba taki ya isa namu na gargajiya ko na zamani, yayin da'a ka kammala jin dadi ya zo, sai mutum ya manta
da wani lokaci ya duka da sunan noma, har sai-shekara ta zago.

Post a Comment

Previous Post Next Post