Magana Jarice: Yaro Bata Hankalin Dare Kayi Suna

Magana Jarice: Yaro Bata Hankalin Dare Kayi Suna

 



A wata kasa nan gabas da nisa an yi wani mutum wanda a ke kira Abdullahi. Yana da samu da yawa, ga shi kuma Malami ne babba cikin dukiyar da ke gare shi har da wadansu rakuma goma sha' bakwai wadanda ya ke zabe, yana saye yana tarawa, dukansu amalai ne girmansu kuwa daya ba yadda zaka ce wannan ya fi wannan Lokacin da ciwon ajali yakama Malamin nan ya ga zai mutu, sai ya kira 'ya'yansa da wadansu shaidu, ya ce, "In na mutu, rakuman nan nawa kada a gama da su cikin kayana da za a raba gado.

Da ma a raina ba don kaina na ke tara su ba. Niyyata in sun yi yawa im ba babban dana nusufi, mai bi masa sulusi, dan autan nan nawa kuwa tusu'insu, to, ga shi ba su yi yawa ba amma duk da haka sai su raba wadanda aka samu hakanan, kada ko wani Malami ya ce zai sake mini abin nan da na yi niyyar yi, ya ce ba-halas ba ne, ni na san abin da na yi nufi a raina." yara suka rungume ubansu, suna kuka.

Can sai suka ji jikinsa ya yi sanyi, su duba sai suka ga ashe har ya cika, ba a sani ba aka tara mutane, aka yi jana'iza, aka gama bayan kamar kwana bakwai alkali ya aiko da Sa'i ya raba musu gado shaidun nan suka gaya masa wasicin da Abdullahi ya yi na rakumansa. da zai raba, ya dobi rakuman nan waje daya, aka raba sauran dukiyar. zai wuce, yaran suka ce, "ai sai ka raba mana rakumammu kuma yadda baba ya yi wasiya, don mu saki hannun juna baki daya.

Abin da a ke kira nusufi shi ne ½ watau rabi abin da a ke kira sulusi shi ne ⅓ watau a raba abu uku a dauki kashi daya abin da a ke kira tusu'i kuwa shi ne ⅛ watau a raba abu gida tara a dauki gida guda sa'i ya yi shiru, ya lissafta rakuma, ya ga yadda uban nan ya bari ba su rabuwa, sai ya ce musu, "Kai samari, rakuman nan ba yadda za a raba su yadda ubanku ya ce, sai fa in za a yanka wadansu a rarraba naman, ko kuwa wadansu daga cikinku su dangana, wani ya dauki abin da ya fi rabonsa ku lura ku gani, rabin goma sha bakwai takwas ke nan da rabi to, yaya za a sami rabin rakumi im ba an yanka shi ba, ko kuwa a sayar a raba kudin? sai fa in sauran sun yarda a cike wa babbanku rabi, ya sami tara.

Saura suka ce, Aa, ba haka baba ya ce ba baba ba ya son wani ya kwari wani, sai ya ce, to, ko kuwa shi ya yar da muku rabi, ya dauki takwas' shi kuma ya amsa ya ce, A'a ni ba na yarda su kware ni baba ya ce kada a sake rabon nan da ya yi" abu duk ya taru ya cabe, sa'i ya rasa inda zai kama, sai ya kwashe su duk da rakuman ya kai wajen Alkali ya kwasne wannan al'amari duka ya gaya masa ko da Alkali ya ji haka, sai ya yi shiru tukun can sai ya ce, to mu fita in ga rakuman." suka fita, ya gan su, ya kidaya, ya kada kai, ya ce, Wannan ai ba wuya.

Samari suka ce, Allah ya gafarta malam, kada fa kowa ya sami abin da ya fi hakkinsa, kada ko kowa. ya kasa. Alkali ya ce, Ku za ku gaya mini A kanku na fara rabon gado? samari suka durkusa, suka tuba. Alkali ya yafe musu sa'an nan ya kira wani bawansa, ya ce, Jeka cikin rakumana, ka koro taguwan nan da na ke hawa. Nanda nan bawa ya zo da ita. Alkali ya ce a gama ta da na samarin nan, aka yi yadda ya ce kowa ya bude baki, ya ga abin da zai yi.

Sa'an nan Alkali ya juya wajen babban, yace, Rakuman nan nawa ke nan? Babban yace, Goma sha takwas, Allah ya gafarta Malam. To, nawa aka ce a ba ka? Saurayi yace, Rabi, Allah ya kyauta aikin Malam, mallam yace Madalla! To, menene rabin rakuma goma sha bakwai?" Saurayi ya ce, "Rakuma takwas ke nan da rabin rakumi, Allah ya gafarta Malam." Alkali, ya ce, To, nawa ne rabin goma sha takwas? Saurayi ya ce Tara,

Alkali yace, In ka sami rakuma tara, kai da ke son takwas da rabi, na ce ko ka wadata?" saurayi ya ce, Allah ya gafarta malam, ai wannan ya wuce wadatuwa. Na sami ribar rabi nan da nan haka? Alkali ya ce, To kore rakuma tara, amma kada ka gama da Tawa na san ko ma ban hana ka gamawa da ita ba, ba ka gamawa don ta fi sauran kankanta, dadi ya kama saurayin, sai ya yi murmushi, ya kora rakuman an tara ya nufi gida da sauri.

Yana tsoron kada rabon ya ki, a ce ya zo ya mayar da daya. sauran kannen saurayin nan sai suka dubi Alkali rai bace, suna tsammani tun da na babbansu ya karu, lalle su nasu zai ragu Alkali ya juya wurin mai biwa babban, ya ce, Kai kuma ne ne aka ce a ba ka? yaro ya ce, An ce a raba uku ne, a ba ni kashi daya, Allah ya gafarta Malam Alkali ya ce, In an raba rakuma goma sha takwas kashi uku kowane kashi nawa za a samu? yaro yace, Allah ya kyauta aikin malam, ko wane kashi za a sami rakuma shida shida ciki, 

Alkali ya ce, Ware shida na ce ko ba a kware ka ba? yaro ya ce, Ina fa kwara a nan ai sa'ad da ba ka ba mu ta ba, rakuma biyar da biyu bisa uku na rakumi zan samu ya kora, ya wuce. Ka san da su fa rakumansu goma sha bakwai ne. Alkali ya sa aka gama da tasa, suka yi goma sha takwas. to, babban ya dauki tara, mai bi masa yadauki shida. to, da tara da shida, in aka tarasu, ka ga goma sha biyar ke nan. In aka debe daga goma sha takwas, saura uku, watau ka ga sauran rakuma uku ke nan aka bari.

Alkali ya dubi auta ya ce, Kai nawa aka ce rabonka? Auta ya ce, An ce in an raba rakuman nan goma sha bakwai gida tara, gida guda shi ne nawa. Watau zan sami rakumi guda ke nan da takwas bisa tara na rakumi, Alkali ya ce, Kai mai son rakumi guda da takwas bisa tara na rakumi in ka sami biyu fa? Auta ya ce, In na sami biyu fa, Allah ya kyauta aikin malam, ai kome ya yi kyau. Alkali ya ce, To, kora biyu, amma ka bar mini tawa. Auta ya kora ya wuce, shi kuma yana murna. Sa'an nan Alkali ya dubi bawan nan, ya ce, Kora taguwata da ka kawo, ka mayad da ita cikin yan uwanta. ya kora ya tafi. Mutane suka yi ta mamakin Alkalin nan bisa ga wannan fasaha.

Post a Comment

Previous Post Next Post