In baku manta a kashi na farko mun tsaya ne inda Dan aike ya sake komawa, ya gaya wa Malam Dan'inna cewa, yayi yayi, wowo ya ki zuwa ya ce kada a dame shi, ubansa ma wanda ya haife shi ya shafa masa lafiya, balle wani da malam dan'inna ya ji haka, sai ya yi salati, hawaye suka zubo masa. ya ce, "koma da gudu, ka gaya masa kudin ubansa malam sidi Ibrahim da aka ga ba su yi auki ba, duk suna nan wajen jaka ashirin, ya binne a wani rami, ni kadai ya nuna wa, ya ba ni amanar in ya shiryu im mika ta gareshi.
READ MORE: Magana Jarice - Girman Kai Rawanin Tsiya Kashi Na Farko
• Magana Jarice Littafi na Farko | Fara Koyon Mulki Da Baki Kafin Ka Koyi Mulki Da Hannu
• Magana Jarice Littafi Na Biyu | In Alllah Ya Taimakeka Kai Kuma Ka Taimaki Na Baya Gareka
To, ga shi har yanzu yana bisa halinsa ni kuwa na ga ciwon nan ba zai bar ni ba, shi ya sa na ke so ya zo in nuna masa abinsa ba wani abu na ke nemansa da shiba, shi ke nan kadai ka rarrashe shi don Allah ya ba zuciya magana ya zo, kada im mutu da wannan amana a kaina ka gaya masa ya san irin wannan al'amari, tun da ya ke ya gama da kudi, bai kamata ba a nuna wa wani, a ce in ya gan shi ya kai shi, ya nuna masa. Na fi so in gan shi ni da shi, ba na son in sa wani tsakani, kada a zo a yi batan bakatantan, ba su ga malam sidi ba su gare shi.
Dan aike ya ruga da gudu, ya tafi ya tarad da wowo bai ko sa ranar tashi ba daga gidan nan ya kira shi waje, don ya gaya masa abin da aka aiko shi a asirce wowo ya ki fitowa sai ya ce ya shigo nan ya fadi, in yana so, in ko da ma sakon bai dame shi ba, ya kama gabansa da dan aike ya ji haka sai ya shigo, ya tsaya gabansa, ya kwashe duk abin da malam dan'inna ya gaya masa ya fadi ko da Wowo ya ji haka sai ya ce, "Haba, na san da ma a rina yadda na san zam mutu, haka na san abin da baba ya bari ya fi goma din abin da muka gada." Sai ya tashi, ya ruga da gudu, ya nufi gidan malam dan'inna, don ya ji kiran nan na samu ne suna isa, suka tarad da malam dan'inna ya cika.
Wowo ya rike kai, ya yi ta kuka har ya tashi zauta ba don mutuwar malam dan'inna ba, sai don bai samu gaya masa inda kudin da ubansa ya bari su ke ba. aka ba shi hakuri, ya dangana da farko mutane sun yi tsammani wannan hasara ta sa ya rage wadansu al'amura, amma af, ko da aka kwana kamar bakwai sai ya ce, "Kai, da ma ba rabo ba, dan wabi ya fada wuta!" Sai ya koma ga sha'aninsa, har ma ya so ya fi da.
Ana nan haka, ran nan bayan an yi kamar wata uku da rasuwar malam dan'inna, sai wowo ya dauki dam molonsa, ya nufi gidan magajiya, ya kunna sigari, yana tafe yana busa ta, ya karkace hula ya kai ta saba'in, sai iskar duniya ke rudinsa, yana tafe yana shegantaka idan mutane suka gamu da shi sai su ratse, don kada ya banke su a banza, su yi salati su ce, "Ba kome, duniya ce, ai ya yi ya bari" wowo yana cikin tafiya, ya kusa kai gidan magajiya, sai ya gamu da wani bakon dan tsoho da gafakarsa
Dan tsoho na tafe dudduke, tsammani ya ke wowo da ya ke yaro ne zai ratse ya ba shi hanya, bai san halin gogan ba ko da wowo ya ga tsohon nan bai ratse masa ba, sai ya tasam masa haikan, ya dauki sanda, ya sa a kafada ya ture tsoho har ya yi taga-taga kamar zai fadi ya mike ya waiwayo ya dubi wowo, ya ce, "samari ba ka gani ne, ka tashi ka kada ni?" wowo ya busa taba, ya shaka, ya dubi dan tsoho, ya ce, "meye ye? je ka, am banke ka, hanyar ta uban waye ye, ba ta sarki bace? "tsoho ya dube shi, hawaye na zuba ya ce, "ni kake zagi? to je ka, ka gani. Daga ni ba za ka sake zagin kowa ba.
Wowo ya waigo da fushi, ya sa hankici ya rufe bakinsa, ya yi tari wai shi akawu, ya ce, "Kurwata kur! mun ci mun sha ba dominka ba. sai dai in ga alheri ka ci kanka, ka sha bakin ruwa, dan neman tsohon kazami!" tsoho ya wuce yana kuka, don wannan bakin ciki ma ko abinci bai tsaya nema ba a garin, sai ya yi gaba Allahu Akbar! In da za ka san girman kai da ashararanci ba abu na gari ba ne, yaron nan bai kulla wata guda ba daga gamonsa da tsohon nan sai da ya haukace. Mutane ba su san yadda aka fara ba, sai ran nan' kawai da hantsi kamar war haka (Allah ya kiyashe mu da aikin war haka), sai ga shi ya fito daga cikin gidansu tsirara, yana sabe da wata fartanya, yana tafe yana caba maganar da ta fito daga bakinsa.
Mutane suka yi ta cewa, "Allah ya kara, da ma mun san a rina, an saci zanen mahaukaciya!" daga ran nan wowo ya haukace, ya yi ta bin gari ba shi da ko wajen kwana sai kasuwa can uwarsa kan rika kai masa dan abinci. In ya shiga gari yawo, da ya gamu da mutum, sai ya ce, "Kai, nuna mini inda ubana ya rufe mini dukiyata!" In ka ce ba ka sani ba, in ya dinga dukanka sai an kwace ka.
Da mutane suka gane, in ya tambaye su sai su ja shi su kai shi wani wuri mai ciyawa, ko a bayan gidansu, ko a kofar gida, su ce, "Ga wurin da malam sidi Ibrahim ya binne maka kudi, jaka dari ne cif, in kana so ka nome wurin nan sarai, ka duba da kyau, lalle ka tono su amma fa don Allah in ka tono ka ba ni kwabo.
Sai wowo ya ce, "to, a ba ka sisin kwabo dai, ai ya ishe ka." sai ya nome wuri kaf, ya yi ta tono, im bai ga kome ba, ya kakkabe fartanyarsa, ya yi gaba, yana cewa, "Wannan bai san inda aka boye ba, karya dai ya ke yi. ba na ba shi sisin kwabon ma da na ce." Haka mutane ke ta wahalshe shi, har rana ta koma ga ubangiji. Allah mai girma!
Dama ance Girman kai rawanin tsiya.