Nan gabas wajen kasashen Barno an yi wani Shaihun Malami, wanda a ke kiransa Malam Sidi Ibrahim. Ilmin da Allah ya zuba masa, da gudun duniyarsa, abin har ba a magana. Saboda haka har mutane na tsammani waliyi ne. Ga shi dai tsohon nan duk inda Shaihun Malami ya kai, ya kai. Amma dansa, inda duk ja'iri ya kai, ya wuce nan. Sunan yaron nan Wowo. Tun yana karami, uban ba irin dukan da bai yi masa ba, har mari ya sa shi, wai don dai ya yi karatu, amma abin ya faskara. Har ya gaji, ya dangana.
Ana nan dai yaro har ya kai shekara goma sha biyar, amma ja'ircinsa sai gaba-gaba ya ke ci Ko ba a gaya maka ba, da ka gammu da shi ka san kan nan da motsi Kullum ya yi sitati, ya sami takalma 'yan ubansu ya soka kafarsa. Ya dauki dankwara ya kafa gaban goshi wandonsa kuwa sai yayi sa- bulanci, ya sabe hannun riga guda kafada waje, ya dauki dam molonsa ya shiga gari yana kwambo. da ya sami kudi sai ya nufi inda a ke sayad da
Giya, ya sha ya yi tatil, ya fito waje yana tangadi, yana fadin abin da ya fito bakinsa. Da mutane sun gan shi ya sha ya bugu, sai su rika yi masa kirari suna cewa, "Wowo dam malam, ka ki halin malam, rago da wutsiyar kare, dam malam, Masallacin kura mai yawan kasusuwa Na-Malam Sidi. Malam na masallaci, kai ko kana dakin bori!" Shi kuwa in ya ji haka sai ya rika gyatsa yana cewa, "Wai! Alheri mu ke bida dai, yaro."
RELATED: Magana Jarice Littafi na Farko | Fara Koyon Mulki Da Baki Kafin Ka Koyi Mulki Da Hannu
• Magana Jarice Littafi Na Biyu | In Alllah Ya Taimakeka Kai Kuma Ka Taimaki Na Baya Gareka
Wadansu kuwa sai su rika ce masa, "Kashin birbiri da faduwada nadewa, yaro ya gani ya ce zobe ne. Sa mai abin ciki da yawa na malam, ga mazawuri ga saifa, ga tumburkuma ga hai.ta." Shi ko bai cewa kome sai, "Yawwa, a gaishe ka dai, samari! Alheri mu ke bida dai, yaro." Yana gabar shakiyanci haka, sai ran nan uban ya kwanta ciwon ajali da ya ga lalle ciwon nan ba na tashi ba ne, sai ran nan ya sallami malaman nan da ke nan gabansa suna jiyya don neman tubarraki, ya ce a kira masa dansa zai yi masa wasici. Aka je aka kira Wowo, ya shiga ya tsaya gaban tsohonsa.
Malam ya kware fuska, ya dube shi, ya ce, 'Kai ne ko, Wowo?" Wowo ya ce, "Ni ne, baba." Uban ya ce, "To, na dai nufe ka da karatu, ka ki, ka zama asharari tsakanin karya da gaskiya. abin da zan gaya maka, kome za ka yi, kai dai ka tsaya ga sa'o'inka, Karatu kuwa tun da ya ke shi ya haife ka, ka ce ba ka so, je ka ka huta. In ka shiryu,
amfanin da za ka samu nan a duniya, balle ma na lahira, ba a magana. Ko ba ka yi karatu ba, in dai
Ka ba zuciyarka magana, ka natsu, ba ka kafirce ba, wallahi yadda arzikina ya shahara nan kasar, kai ma sai ka kai hakanan," Sai ya sa mayafi ya rufe kansa, kamar barci ya dauke shi. Ashe har ya cika da aka farga da haka, aka tafi aka gaya wa Sarki da dukan jama'a, suka taru wajen jana'iza. aka yi aka gama.
Jama'a sun gama addu'a, za su watse, sai daya daga cikin malaman nan da Malam Sidi Ibrahim ya ce su dakata sa'ad da zai yi wa dansa wasici ya matsa, ya ce wa Sarkin garin, "Ai ko da malam zai cika, ya yi wa Wowo wasiya, ba'a tambayarsa, a ji abin da ya fadi?" sarki yana tsammani ko ya yi wasiya da wata magana ce da malamin nan ya ga ya kamata a gaya wa jama'a, saboda haka ya dubi Wowo, ya ce, "Me malam ya yi ma wasiya? Yaro ya ga ba abin da ya gama malamin nan da abin da mahaifinsa ya gaya masa, har da zai ce sarki ya tambaye shi ya bayyana wa taro. saboda haka ya dubi Sarki, yace,
"Allah ya ba ka nasara, abin da ya gaya mini bai kamata ba a bayyana, don kada mutanen da ke nan hankalinsu ya tashi." Sarki ya ce, wane abu ne haka da ka ke tsoron fadi? ai gwamma ka fadi nan gaban jama'a, kowa ya san abin da a ke ciki Wowo ya ce, "Allah ya daukaka ka, ya fi kyau a bar kaza cikin. gashinta.'"
Sarki ya ce, "A'a, tun da ni na tambaye ka, ai sai ka fadi. In yunwa ce ya ce za a yi, ka fada mana mu yi tanadin hatsi. In ko annoba ya gaya maka za ta auku, ya fi kyau ka bayyana mana, munai mi hatsi" wowo ya ce, "Duk bai fadi daya daga cikin wadannan ba."
Malamin nan da ya takalo maganar ya ce, "sarki ke magana da kai gaya masa abin da aka bari mana, ka tsaya kana noke-noke, kamar kana magana da tsaranka?" wowo ya dubi sarki, ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ba banza ba na ke noke-noken fadi. Cewa ya yi in an gama jana'izarsa, duk wanda ya fara mikewa tsaye a wurin, bayan kwana bakwai zai bi shi abin da ya sa ya gaya mini kuwa, don ni kada in fara tashi." mutane da jin haka fa, sai wannan ya dubi wannan, wannan ya dubi wannan, Sarki ya dubi Liman, ya ce, "Liman, ai sai ka tashi mu tafi.
Liman ya ce, "A'a! In tashi? Ai kai ne babba, fara tashi mana, mu ko mu bi ka daga baya." da yaran da ke nan suka ga manya sun yi zaune, an rasa mai fara tashi, kowa na kallon kowa, sai suka yi ta rarrafe, suka nufi gidajensu suna cewa, "Tsaye dai aka ce ba a tashi. To, ba mu tashi ba. Da Sarki da jama'a da suka ga yara sun yi rarrafe, sun tafi gida jensu sun huta, sai su kuma kowa ya janjanye bujensa. sarki ya wuce gaba da rarrafe, sauran jama'a na biye har suka kai shi gida sa'an nan kuma kowa ya rarrafa zuwa gidansa sauran yaran da ba su kai ba suka yi ta bin dattijan nan, suna yi musu dariya.
Bayan kwana bakwai aka zo raba gadon abin da malamin nan ya bari abin ya zo da sauki, don malamin bai bar wani mai gadonsa ba, daga dansa Wowo sai matarsa uwar yaron da aka fidda dukiyar da ya bari aka raba ta takwas, aka dauki kashi guda aka ba matar, saura kuwa aka ba wowo, don haka shari'a ta ce a yi.
Da aka gaya wa mai garin yawan abin da sidi Ibrahim ya bari, sai ya yi mamaki kwarai da gaske yadda abin ya karance haka da mutane na tsammani a kalla ya bar biyar din abin da aka iske asher ko suna da gaskiyarsu. Sa' ad da Malam Sidi Ibrahim ne ya ga ya tsufa, ya sami akwatin karfe, ya gina rami a wani wuri, ya kwashe kudin da ke gare shi duka ban da kaddara, ya kai ciki ya kulle da ya ga ya kwanta ciwon nan na ajali, ya kira wani amintaccen almajirinsa dan'inna, ya nuna masa wurin, ya ce masa, "Ga amanar Allah da Ma'aiki nan na ba ka.
Domin ka san rai kwakwai, mutuwa kwakwai In Allah ya sa na riga ka mutuwa, ina son ka ba Wowo su. Amma kada ka gaya wa kowa wannan al'amari, ko shi yaron kuwa ma kada ka nuna masa ko alamar akwai wadannan, sai ka ga ya shiryu. Ka san in ya san da su yanzu a wannan hali nasa, cikin kwana bakwai yana iya fallasad da su duka, ya koma ga sa ido wajen mutane, ana yi masa gori "dan'inna ya ce, "na ko karbi wannan amana taka, malam. Annabi kuwa ya zama alkali tsakanimmu, in wani rashin gaskiya ya auku bisa ga wannan amana." To, duk wannan al'amari ba wanda ya san ya auku sai su biyu kadai da suka yi abinsu, har rasuwan nan ta Malam Sidi Ibrahim tazo.
Bayan ya rasu, Malam dan'inna ya yi ta kiwon Wowo da ido, ko ya ga ya yi dan sanyi-sanyi ma bisa ga irin halinsa, ya nuna masa dukiyar, ya fid da kansa Bai ga ya yi ba maimakon ma ya kara raguwa, sai haukata abin nasa ke kara yi. tun Limamin garin na kiransa na yi masa fada, yana ba shi magana, har ya gaji ya kyale shi, Ana nan bayan mutuwar Malam Sidi Ibrahim da shekara biyar, malam dan'inna ya kwanta ciwon ajali Yana nan kwana da kwanaki, sai a kwantar a tayar ran nan da ya ga dai alamar ciwon nan ba zai bar shi ba, sai ya ce a ransa, "Ya kamata im ba wowo kudinsa, don kada im mutu in yi masa hasara da wannan ko ya auku, ai gwamma in nuna masa abinsa, in ya so in ruwa zai zuba ya zuba" Ya aika a kira wowo.
Da aka tafi, aka tarad da shi gidan magajiya, yana kidan molo aka gaya masa malam dan'inna na kiransa maza-maza sai ya dubi manzon haka yatsine, ya sa sigari da ke hannunsa a baka, ya ja, ya hura hayaki ya fito ta hanci da ta baki, ya ce, "Kai samari, je ka ka gaya masa ban bugi dan kowa ba, ban zagi dan kowa ba, ban ga abin da ya gama shi da ni ba da zai aiko yana kirana da sauri haka. "Dan aike ya ce, "Ai ko yana nan rai ga Allah, gwamma ka tafi,watakila wani abu zai gaya maka" wowo ya harare shi, ya sake sa sigari baka ya ja, ya ce "Kai, don Allah tafi ka raba ni da wuya. Af, ya je ya mutu mana! Wane abu ne zai gaya mini wanda ubana bai gaya mini ba "dan aike ya sake komawa, ya gaya wa Malam Dan'inna.
• Muhadu a kashi na 2 Domin jin yadda zata kaya.