Akwai Rashin Kwanciyar hankali bayan tarzomar Watan mayu. Akwai rashin tabbas a kan me zai Faru da dokar soja ta talatin da hudu da rashin Kwanciyar hankali da zarge-zarge a rundunonin Soja, An kawar da hanyoyin sadar da umarni kamar yadda yake a ka'idojin aikin soja.
Katsahan sai ga sanarwar sauya wa gwamnonin Jihohi gauraren aiki da nadin (Prefects-Prefects) Na soja. Wannan ya dada rura guguwar rashin Zaman lafiya da Rashin Amincewa a cikin soja, An baza jita jitar cewar aikin da aka fara na 15 ga watan Janairun 1966 da ba'a kare ba yanzu
Za'a ci gaba (kisan manyan 'yan siyasa da hafsoshin soja 'yan arewa).
ALSO READ: Mulkin Soja: Kifar Da Gwamnatin Ironsi A Nigeria
• MULKIN SOJA: Hawan Birgediya Murtala Ramat Mohammad Shugaban Kasa
• Mulkin Soja: Mulkin Shugaban Kasa Janar Gowon Da Alkawarin Dawo Da Siyasa A Shekarar 1976
Akwai jita-jitar juyin mulki na ramuwar gayya daga Sojoji 'yan Arewa da taimakon farar hula Ranar 28 ga Yulin 1966 akwai almu da suka nuna Wannan bangare ko wancan yana neman yin Wani abu amma cikakken bayani bai samu ba ga manyan hafsoshi a hedikwatar hafsoshin.
Majalisar koli ta soja (Supreme Head Quarters) da majalissar Soja (Army Head Quarters) sun dauki Matakan da ya kamata su dauka na jan hankalin Rundunonin soja da su Zauna Cikin Shiri. Daga binciken farko da aka yi wani hafsa a abeokuta ya dauki matakin da ya wuce na zama cikin shirin ko ta kwana.
Domin bada makamai ga hafsoshi da sojoji yan kudancin kasa da ya yi. Yayin da sojoji 'yan arewa Suka samu labarin wannan abu ya ba su tsoron kada a maimaita abin da ya faru a ranar 15 ga Janairun 1966 Miladiyya, don haka suma sai suka Dauki makamansu.
Wadannan 'Yan arewa sai suka harbe hafsoshinsu uku nan take, kuma fadan cikin gida Ya barke a cikin rundunonin soja da ya bazu zuwa Ibadan, Ikeja da sauran bangarori da ke arewa Na Soja. Wannan tashin hankali ya barke duk tsahon kwana biyu na karshen watan yuli, Inda aka kama tsohon kwamandan koli na soja Janar Ironsi da Gwamnan soja na Ibadan Fajuyi a gidan Gwamnati dake Ibadan.
Bayan wadanda suka mutu ranar 15 ga watan janairu da 29 ga Yulin 1966 miladiyya an samu cewa mafi yawan wadanda suka rasa rayukansu Hafsoshin sojoji 'yan kudu maso gabashin Nigeria ne, Kamar dai kishiyar abin da ya faru ranar 15 ga Janairu inda ba 'yan kudu maso gabas ba ne aka kashe Abubuwan da suka faru da tattaunawar da akayi da har ya jawo Lt. Col. Yakubu Gowon ya zama shugaban gwamnatin mulkin soja kuma babban kwamanda a Majalisar Koli,
Wannan shi ne bayanin Gwamnatin Mulkin Soja ta tarayyar Nigeria a karkashin sabon shugaban kasa Kanar Yakubu Gowon. Ranar 27 ga mayun 1967 kanar Gowon ya sanar da kafa dokar ta baci, da kirkiro sabbabin jihohi, sannan ya yi kira ga rundunar sojojin kasa domin shirya tunkarar Tsohon Gwamnan kudu maso gabas Kanar Ojukwu da ya fara yin shirin tawaye a watan yuni 1967 miladiyya.
Gowon ya nada kwamishininin tarayya a majalisar zartarwa ta kasa wanda suke mafiya yawa farar hula ne, 'Yan Arewa a wannan sabuwar majalisar zartarwa sune kamar haka, Aminu kano, Shattima Ali Manguno, Dr. R.A.B Dikko, Joseph Tarka, Dr. Adetoro, Yahaya Gusau.