Za'a Fara Dashen Bargo a Asibitin Koyarwa Na Aminu Kano AKTH - Farfesa Abba Sheshe

Za'a Fara Dashen Bargo a Asibitin Koyarwa Na Aminu Kano AKTH - Farfesa Abba Sheshe

 



Asibitin koyarwa na Aminu Kano, da ke jihar ta Kano, a ranar  Litinin din da tagabane aka kaddamar da wani sabon sashin kula da cututtukan jini kuma hakan ya nuna cewa za a fara dashen bargo a Asibitin.

Aminu Kano Teaching Hospital  zai kasance asibitin koyarwa na biyu a Nijeriya da zai rika yin dashen bargo a kasar Nigeria Babban Daraktan Asibitin Farfesa Abba Sheshe ne ya bayyana haka a wurin kaddamar da cibiyar a hukumance, wanda wani Injiniya mai suna Umar lbrahim ya bada ita a matsayin gudunmawa.

Ya bayyana cewa asibitin koyarwa na jami'ar jihar Legas ne kadai ya yi nasarar dashen bargo a Najeriya Ya kuma jaddada cewa kayan aikin da za a sanya a cibiyar za su sanya a samu nasarar
dashen bargo a asibitin.

Ya yabawa mai bayarwa lbrahim, kuma yayi addu'ar Allah ya saka masa da alkhairi.
Da yake jawabi a madadin mai bayar da
tallafin, Farfesa Mahmoud Daneji, ya ce an yi hakan ne domin tunawa da marigayiya mahaifiyarsa.

Post a Comment

Previous Post Next Post