Yadda Ake Wasan Gauta A Kasar Hausa

Yadda Ake Wasan Gauta A Kasar Hausa

 



Wasan gauta wani irin wasa ne da ake yi na kwaikwayo dan mutane su san yadda abubuwan mulkin kasa suke gudana a cikin kasa baki daya da kuma yadda huldar mulki take.

Wannan wasa ana yinsa ne da kaka lokacin da kayan gona suka zo wato lokacin da suka cika gari. Dalilin ma da yasa ake gaya masa wasan Gauta, saboda gauta shine kamar goro a cikin wasan, Duk wanda ya dace a bashi goro sai a bashi gauta.

RELATED: Takaitaccen Tarihin  Makarantar Gidan Makama | Makama Special Primary School kano

• Tarihin Rikicin Marwa Mai Tatsine A Kano Da Wasikar Da Gwamna Abubakar Rimi Ya Turawa Mai Tatsinen

A cikin wannan wasa a kan kamanta sarautu da yawa da mukaman aikin gwamnati, wato dama wasan kwaikwayo ne na yadda ake tafiyar da mulki irin na gargajiya da kuma yadda  ake tafiyar da hukuma da kuma aikin hukuma na yau da kullum.

Cikin abubuwan da ake kamantawa akwai sarakunan yanka irin su sarkin musulmi, sarkin katsina da sauransu, akwai hakimai da alkalai.

Akwai su yarin kano, akwai sittar Asibiti da su sarkin aiki kai har a wata shekara ma an taba yin sakataran majalisar Dinkin Duniya amma a Chiranci aka taba yi lokacin sarki Sunusi ya ke Chiranci.

Kafin a yi wannan wasa sai an zauna an tsara yadda duk za ayi da Sarautun da ake son ayi da wadanda za su kwaikwaye su sa'annan sai a fadawa Sarki don neman izininsa da taimakonsa, Yawanci ma'akan mutumin da za a din ko yana sha'awa zai turo iyalinsa su yi kallo wannan wasa yana da kayatarwa.

Abin sha'awa har da wakilin doka da yan sanda suma sukan kama wadanda aka ga zasu kawo rudu ko tashin hankali. Akan aro kayan aiki ko a dinka sababbi Amma rigunan Sarakuna da na hakimai Sarki ne yake ba da aro ko a dinka sababbi.

Wannan wasan akan yi shi ne a filin sararin Garke, A wannan fili ne za ayi amfani da karagu da asabari da su gadon kara wani ma har a kakkafa azaru da tukware ko wane gida akan fitar da shi ko wacce ma'aikata ita ma a fitar da ita.

Wannan wasa na gauta akan yi kamar sati biyu ana yinsa mutane kuma daga birni da kauye su yi ta zuwa suna kallo, Sarakunan da aka aikawa cewar za'a kwaikwayesu, suma sukan aiko da mutane har da abin hasafi.

Ma'aikatu kuma da akan kwaikwaya yawanci kuyangi ne suke yi domin su dama suna fita waje saboda haka yafi musu sauki su je su karbo kayan aiki aro ayi wasan daga baya su mayar musu. Kuma idan zasu aro kayan aikin asibiti sai sun je an nunnuna musu yadda ake amfani da kayan, ko wanne kuma da sunansa kun ga ashe wannan wasa karamar hanya ce ta ilmantar wa a wasance ba kowace maceda ta zo kallon wannan wasa sai ta fita da dimbin ilmi na aikace-aikace da shari'a.

Post a Comment

Previous Post Next Post