Tun a zamanin Kano ta dauri anbawa magudanan ruwa muhimmmanci, wanda yana daga cikin tsarin manyan birane a faɗin duniya. Ko a wancan lokaci, an tsara birnin Kano daidai da cigaba na wancan lokaci, bisa hasashen ƙara faɗaɗa gari ba tare da wata matsala ba.
Wannan hoto Lorennzo Dow Turner ya dauke shi a shekarar 1951. Daga ƙarshen hoton, za ka iya hango sinamar Palace. Babban abin da ya ja hankalina a hoton shi ne wannan babbar magudanar ruwa, wanda ta ratsa Jakara. Ita ce za ta haɗe da babbar kwatar Kwarin Gogau, sannan ta yi gaba zuwa ruwan Kwakwaci.
READ MORE: Takaitaccen Tarihin Makarantar Gidan Makama | Makama Special Primary School kano
• Tarihin Masarautar Kano Daga Mulkin Maguzawa Zuwa Fulani
• Takaitaccen Tarihin Sarki Alhaji Abdullahi Bayero
A wannan zamani da Kano ta ƙara bunƙasa, manyan gidaje na alfarma da ma'aikatu suka ƙaru, abu ne mai wuya ka ga manyan magudanan ruwa, wanda za su tafi da zamanin da ake ciki. Kai, ya zamanto ma gine hanyoyin ruwan ake ba tare da tunanin inda za a kaɗa ruwan ba. Wannan yake janyowa ana samun ambaliyar ruwa a Kano.
Kar ka so ruwa mai ƙarfi ya same ka a waje, domin idan ranka ya yi dubu sai ya ɓaci. Kwalta ce za ka ga ta shafe, wanda kana cikin mota ko a kan babur, ko a ƙasa kake sai da dabaru. Sai kuma garin ya cunkushe, kamar ana wani babban sha'ani. Idan ka yi rashin sa'a kuma, sai ka dawo gida ka tarar ruwa ya ci unguwarku.
Yanzu dai a wannan damuna, mun ji yadda ruwa ya ci mutane a cikin tsakiyar birnin Kano. Wasu suna kan abin hawa, wasu ma dai sai dai a ga ruwa ya jawo gawarwakinsu. To, ta yaya za mu samu sauƙin wannan ambaliya alhali ba mu ɗaura daga inda magabata suka tsaya ba. Ba a maganar hanyoyin ruwa na ƙarƙashin ƙasa da muke kallo a Turai, bare irin na gargajiyar da muka gada. Wannan matsala ba ta tsaya ga hukuma ba, bare mutanen gari da ke gine-gine ba bisa ƙa'ida, sannan ba tare da gina koda ƙananan kwatoci a gidajen su ba.