Tarihin Rikicin Marwa Mai Tatsine A Kano Da Wasikar Da Gwamna Abubakar Rimi Ya Turawa Mai Tatsinen

Tarihin Rikicin Marwa Mai Tatsine A Kano Da Wasikar Da Gwamna Abubakar Rimi Ya Turawa Mai Tatsinen

 



An haifi Marwa Maitatsine a cikin shekarar 1924. Kodayake a iya bincikenmu ba mu gano ainihin iyayen maitatsine ba, amma bincike ya tabbatar da cewa, Marwa Maitatsine Mutumin kasar Kamaru ne,  amma Mai tatsinen yana ikirarin cewa shi mutumin k'auyen Jabbi ne wacce take cikin tsohuwar jihar Gongola, a yanzu jihar Adamawa.

Yana boyewa da jihar Gongola ne saboda yadda yake sarrafa harshen Fulatanci, amma da aka zurfafa bincike an gane Mai tatsinen  karya ya yi Maitatsine dan wani kauye ne mai suna Jappa A arewacin kasar kamaru, garin yana kan iyaka tsakaninsu da Nijeriya.

Shi Mai tatsine dan kabilar Mufu ne wadanda mafi yawansu ba Musulmai ba ne, Ba su da addini maguzance suke bi, Maitatsine ya shiga addinin Musulunci a cikin shekarar 1940 A lokacin yana dan kimanin shekaru16 a duniya,  A wancan lokacin ya bar kauyansu ya nufi Marwa. Garin marwa, gari ne na 'yan kabilar Mufu, kafin Fulani su zo su mamaye shi,  Shi ya sa fulatanci ya zama shi ne harshen mutanan garin.

Har Maitatsine yakai fiye da shekaru 16 yana muguwar al'adar nan ta tsafi, da bautar gumaka, amma Maitatsine bai bar bautar gunki ba, da duwatsu. Suna dinka kambuna da manyan layu,  Ga su da irin kau-da-bara, da sagau, ga su da cin bakin tauri, wuka ba ta kama su.

Sukan yanka ma Dodo, dan Adam ma'ana su ma sukan zubar da jini Irin wadannan tsafe-tsafe da camfe-camfe, Maitatsine ya taso da shi, ya kuma rika yi har da ya zo Kano, Maitatsine ya fara zama yaron gidan wani Balarabe ne mai suna Mohammad Arab, wanda shi ne ya musuluntar da Maitatsinen bayan bayyanar Maitatsine, da yawan mutane sun dauka sa'a ta yi kusa, tunda Dujal ya bayyana, rana kawai suke jira ta fito ta yamma, ta fadi a gabas.

Maitatsine bak'i ne tsamurarre mara jiki, tsawonsa zai kai mita 1.7. Sannan ba shi da tsage a fuskarsa, yana da hakorin gwal guda biyu a bakinsa. ya sa shi ne a Makka a shekarar 1970. Maitatsine, ya isa Kano ne, cikin shekarar 1955, nan da nan kuma ya fara wa'azi.

ALSO READ: Takaitaccen Tarihin Sarki Alhaji Abdullahi Bayero

• Tarihin Abubakar Imam Marubucin Magana Jarice Da Nasarorin Dayasamu A Rayuwarsa

• Tarihin Masarautar Kano Daga Mulkin Maguzawa Zuwa Fulani

Bayan farko-farkon samun yancin Nijeriya, lokacin ne sha'anin na Maitatsine ya fara ta'azzara. Lokacin hankalin Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Sir Muhammadu Sunusi ya juyo kan Mai tatsinen Sir. Sunusi ya sa aka fidda Maitatsine daga Kano, bai ma tsaya nan ba. Sarkin sai da ya tabbatar da cewa an mai da shi kasarsu ta Kamaru a cikin shekarar 1962. Bayan da Maitatsine ya koma can kasarsu ta Kamaru ya ci gaba da yada wannan barna, yana badala.

Bayan Marwa na wancan lokacin Lamido Yaya Hammadi ya kore shi cikin shekarar 1963, ya sake Dawowa garin Kano, bayan murabus din Sir. Sunusi,  mai tatsune ya komo kano da akidar Qur'ani Zalla. Maitatsine yana da'awar shi Annabi ne, kuma yana ganin kansa kamar mujaddidi Shehu Usman dan Fodio.

Maitasine yana da akidar Qur'ani Zalla, yana inkari ga hadisi da sunnar Manzon Allah (SAW) kuma yana hani ga karanta wani littafi in ba Qur'ani ba, Maitatsine yana ganin aiki da kayan bature haramun ne kamar su radio, agogo, kekuna, motoci da sauran su.

A shekarar 1979, ya fara wannan da'awar ta shi Annabin hausa ne a 'yan tsakanin shekarun 1978 zuwa1979 din ne 'yan sandan Nigeria suka sake kama shi. Sannan aka kama yaransa wato yan Tatsine.

Rundunar sojojin Nigeria ta ba da sanarwan kimanin mutane dubu biyar 5,000 ne suka rasa rayukansu a rikicin Maitatsine cikin har da shi kanshi Maitatsinen da jama'arsa.
Maitatsine ya mutu sakamakon wani rauni da aka yi masa, wasu kuma sun ce ciwon zuciya ne ya kashe shi.

Wasikar Gwamna Rimi Zuwa Ga Marwa Mai Tatsine A Kano

Gwamba Rimi ya fara da cewa labari ya iso garemu cewa, kai  Marwa, ka mallake wasu filaye a unguwar yan' awaki cikin birnin kano ba bisa kaida ba, kuma har kayi gine gine ba tare daka sami izinin yin hakan ba daga wajen hukumomin dake bayar da izini, hakanan kuma an shaida mana cewa daruruwan mabiyanka suma sun mallake wasu filaye inda suke gina makwanci
ba tare da sun nemi izini daga gwamnatin
kano ba, sannan an bamu labarin cewa,

Mabiyanka suna da bindigogi tare da muggan makaman da suke fito dasu a fili kowa na gani, Na tabbata kasan cewa wadannan abubuwan dana lissata dukkansu sun karya dokokin kasa da gwamnatin kano, kuma dai kasan bazamu zuba maka idanu ka cigaba da aikata irin hakan ba.

Game da wadannan abubuwa da aka lissata
a sama, ina sanar dakai cewa, na baka
makwanni biyu daga yau, akan lallai rushe
gine ginen da kayi ba bisa kaida ba, ka kuma
tashi daga wajen kacokan.

Suma mabiyanka ka basu umarnin su rusa
dukkan gine ginen da sukayi da kafe kafen da sukayi na bukkoki kuma subar wannan
yankin gaba daya, ina yi maka matsanancin
gargadi akan cewa lallai kayi aiki da wannan magana, mutukar kayi kunnen uwar shegu da maganar, kaki yin aiki da ita, to kuwa ba zaayi wata wata ba, illah kawai gwamnati tq zabi daukar duk wasu matakai da suka dace akan lamarin.

Bugu da kari, bayan wadancan miyagun
abubuwan da kake aikatawa na karya doka
da oda, hukumomin kare doka tare da
mutanen dake zaune a unguwar yan' awaki
sun sanar dani cewa, mabiyanka suna cin
zarafin bayin Allah, sannan suna aikata wasu boyayyun laifuka, kwanan nan akayi arangama tsakanin yan sanda da mabiyanka wanda har takai da rasuwar dan sanda guda daya da kuma farar hula guda biyar, na.lura da cewa babu alamar ka dauki matakin hana mabiyanka ci gaba da aikata wadannan miyagun laifukan, saboda haka ina kira gareka da kuma dukkan mabiyanka, akan ku tattara naku ya naku ku bar unguwar yan' awaki nan da kwana goma sha hudu masu zuwa, idan kuma kuka ki to gwamnati zatayi abun daya dace akai.

Ina kara jan hankalinka akan cewa kai da dukkan jama'ar ka baku da ikon daukar doka a hannunku, ina kuma kara tabbatar maka da cewa gwamnati ba zata zuba maka idanu kai da mabiyanka ku dinga cuskunawa jama,a ko tayar musu da hankali ba, ina kara shawartarka da kwakkwarar murya akan lallai wannan gargadi nawa ya shiga kunnen ka, kuma kai da mutanenka lallai ku rushe dukan gine ginen da kukayi ba bisa kaida ba, kuka ku bar yankin cikin wa'adin da muka baku.

Na aika da kwafin wannan takardar zuwa ga
shugaban kasa Shehu Shagari, Sufeto janar
na yan sanda Alhaji Adamu Sulaiman, kwamishinan yan sanda na jihar kano, mataimakin darektan kungiyar tsaro ta kasa dake kano, shugaban majalisar dokokin jihar kano da kuma babban jojin jahar kano, domin su sani su kuma dauki matakan da suka dace a nasu bangaren.

Post a Comment

Previous Post Next Post