Takaitaccen Tarihin Sarki Alhaji Abdullahi Bayero

Takaitaccen Tarihin Sarki Alhaji Abdullahi Bayero


 


Alhaji Abdullahi Bayero shi dan Sarki Abbas Maje Nasarawa ne dan Abdullahi Maje Karofi ne shi An haife shi a shekarar 1299 Hijiriyya daidai da 1881 Miladiyya kamar yadda Mallam Husaini Sufiya ambata a cikin littafinsa mai suna "Mu san Kanmu."

Alhaji Abdullahi Bayero ya yi makarantar Allo a wajen wani malami da ake cemasa malam lsyaku na bakin Shahuci. Bayan yayi aure da shekara daya Turawa suka shigo Kano zamanin Sarki Alu Mai Sango dan Abdullahi Maje Korofi wato wan mahaifinsa.

RELATED: Tarihin Masarautar Kano Daga Mulkin Maguzawa Zuwa Fulani

• Canje  Canjen Mulki a Arewa  Bayan Rasuwar Sardauna

Mahaifinsa Abbas Maje - Nasarawa ya hau kan gadon sarauta bayan Alu ya bar Kano lokacin da Turawa suka zo, a wannan zamani ne aka nada Abdullahi Bayero Chiroman Kano 1321 Hijiriyya,
1903 Miladiyya. Bayan nan kuma ya taba yin Wazircin Kano bayan ya yi aka kai shi garin Bichi ya zama Hakimin Bichi.

Daga nan aka nada shi Sarkin Kano na goma a ranar sha biyar ga watan Shawwal 1344 A.H (26/4/1926). Sarki Alhaji Abdullahi Bayero ya yi ayyuka da yawa dangane da ci gaban kasar Kano kusan mu ce ayyukan da ya yi ba'a taba samun
Sarki a Kano da yayi irinsu ba kafin zuwansa kan gadon sarauta.

Sarki Alhaji Abdullahi mutum ne mai farin jini mai son zaman lafiya da kowa, mai son addini da neman ilimi na kowane fanni, mai karbar baki da abubuwan da zamani ya kawo muddin dai ba su saba ka'iar dar shari'a ba. Sarki yana son malamai da gaske don haka ma sune abokan shawararsa a ko yaushe.

Ance takanas yakan tashi ya tafi gidan Malami don fatawa maimakon yayi amfani da mukaminsa na mulki ya aika a kirawo malamin ya zo fada. Wadannan malamai da Sarki yake hulda da su sun yi tasiri kwarai a kan yadda Sarki ya dage ya dinga kirkiro makarantu yana tsayawa a kansu.

A zamaninsa an sami cigaba a fanni - fanni na kyautata rayuwa, misalin irin abubuwan sune ruwan fanfo, lantarki, asibiti na mutane da na dabbobi, ma'aikatar tsabta da dai sauransu,
Sarki yaje makka aikin hajji da iyalinsa a shekarar 1937 miladiyya wanda ya yi dai dai da 1354 hijiriyya.

Post a Comment

Previous Post Next Post