Takaitaccen Tarihin Makarantar Gidan Makama | Makama Special Primary School kano

Takaitaccen Tarihin Makarantar Gidan Makama | Makama Special Primary School kano

 



Makarantar Makama ta kasan ce makarantar Boko ta farko da yayan Sarki suka fara zuwa an bude ta ne a wani gida da ake cewa da shi Gidan Makama, Gidan Makama wani tsohon gida ne wanda Sarki Muhammadu Rumfa ya fara zama lokacin yana sarautar makaman kano.

An bude wannan makaranta a shekarar 1930 miladiyya, to da aka bude ta sai Sarki ya debi yayansa hudu rak da yake dasu a wan cen lokacinharda mahaifiyar Rabi Abubakar Wali  wadan nan yara sune Saude wadda ake cewa da ita Fulani Goggo, sai Aishatu wadda ake cewa da ita  Fulani Atukku, sai Zainab wadda ake cewa da ita Fulani yarriga.

Kullum da sassafe sai a saka jakadiya Lamunde ta raka su makarantar bokon, bayan Sarki ya saka yayansa hudu sai sauran hakimai ma dole suka fito da nasu yayan Waziri Gidado yasaka Zulai da Nafi, Galadima ya saka yayansa biyu da bacucanyarsa daya, Amina, Tafada, da Habi, madakin kano ma ba'abarshi a baya ba ya kai su Gambo da Delu da Ramatu wadanda daga baya har sun yi aikin asibiri.

Har Gambo da Delu suka zama sittotin asibitin Murtala.Akwai ma barorin alkali ja'afaru suka yargoggo da sabuwa wan nan makaranta yini ake yi sur har sai dare yayi a dawo gidan Sarki a kwana gobe a koma Malaman wannan makaranta Turawane Sunan shugabar makarantar Miss pegen, akwai kuma wata baturiyya miss pendle.

A wannan makaranta ana koyar da Turanci da Lissafi ya yin abinci da sana'o'in hannu iri-iri ana koyar da yadda ake kula da gida da renon yara. Daga baya da aka amfanin wannan makarantar sai nan da nan ta cika.

Da farko kuwa harkuka aka ringa yi kamar musiba ta abku ana cewa an debi yara an kai makarantar  turawa, suma yaran idan zasu tafi sai iyayen goyensu su ringa cewa da su "kada fa ku ringa kula da abinda suke koya muku, kuma kome suka baku kada ku ci."

Wani lokacin galadima Abdulkadir yakan je makarantar ya gansu ya ringa basu hakuri yana cewa ku yi karatun babu komai ai Sarki ba zai kawo ku nan ba idan ya san akwai illa, kuma idan ya samu an  basu wani abu irin na turawa sun ki ci sai ya ce ai babu komai bari ma ku gani, sai ya dan diba yaci, yace kungani nima na ci ai sai ku ci, ai sai  kuci, Haka dai aka zauna a Makarantar Gidan Makama ana dari-dari da Turawa.

Post a Comment

Previous Post Next Post