Takaitaccen Bayani Akan Sanar Dukanci a Kasar Hausa | Dukawa

Takaitaccen Bayani Akan Sanar Dukanci a Kasar Hausa | Dukawa

 



Dukanci dai sana'ace da ta samo asali daga jima, yayin da majema su ka sarrafa fata, ta zama fata sosai jemammiya, lokacin dukawa za su sayi fatun dan amfani da su.

Allah yayiwa wa su dukawa, baiwa domin akwai hikima a cikin lamarin, daga yadda mutum zai daga fata, fakaka, ita ba zani ba ita ba mayafi ba. 

ALSO READ: Takaitaccen Bayani Akan Sana'ar Dinkin Hannu Da Dinkin Keke A Kasar Hausa

• sana'ar Jima a Kasar Hausa | Majema

• Asalin Sana'ar sassaka a Kasar Hausa | Masassaka

Amma haka baduku zai dauki fatar nan ya sarrafa ta yadda yake so, wani lokaci a yi jaka babba ko karama, Ga takalma da ake yi banda wasu suturun  da akan hada su da fata kamar malfa, warki, da sauran wasu abubuwan rayuwa.

Ana sarrafa fatar wajen yin abubuwa daban-daban kamar gafaka, rufin laya zuwa kan gidan wuka ko kotar takobi, zugi-zugu da dai sauran abubuwa na rayuwa da dukawa kan taimaka ta bangaresu.

Post a Comment

Previous Post Next Post