Sana'ar dinki ba ta da wa ta wahala ga dukkan mutumin da ya sa kansa, don in ka duba duk da son jiki irin na mata za ka ga wasu masu himma acikin matan sun rike sana'ar diki hannu bi-buyu saboda alherin da suke samu da albarkar sana'ar.
sana'ar dinki tana da fadi da yalwa a cikinta. wannan sana'a ada kafin zuwan turawa, muna da madinkan mu,wanda suke samar da kayan maza kamarsu rigar saki da bunjuma da wundiya da garken nufe da shabka da rigar tsamiya da bala-kura da sace-kan-adda da aska da cibiyar kura.
READ MORE: sana'ar Jima a Kasar Hausa | Majema
• Takaitaccen Bayani Akan Sana'ar Su | Kamun Kifi
• Asalin Sana'ar sassaka a Kasar Hausa | Masassaka
Akwai kuma wanduna suma ana dinkawa ko kuma ayi musu aiki duk da hannu, kamar su wando mai kamun kafa da wandon tunus da kwarjalle na fari da bandama.
Akwai kuma kayan mata wanda suka hada da alkillada bun da zanin saki da mayafi da dunhu da dantofi da sauransu muna da huluna kamarsu habar kada da saki da bakwala da sauransu. wannan sana'ar ba wani kayan aiki mai wuya ne da sana'ar ba, allura da zare sune jarin mutum sai kokarin yin dinki.
Shi kuma Dinkin keke,wata hanya ce Mai sauki da ta bullo ma na da ga baya, ta amfani da keken dinki maimakon amfani da hannu, Dinkin da zai dauke ka wata guda a na yi, a kwana guda za'a iya gama shi, yadda mata da maza su ke dinkin hannu, hakama dinkin keke, sai dai keken ya na bukatar almakashi.
Saboda ana amfani da shi, don yanka yadi wajen siffanta yadda ake bukatar dinkawar kayan maza ko mata, kuma yanzu wani karin birgewa har aiki na mu na gargajiya ake yi da keken dinki. Sai dai yawanci aikin da a kan yi da hannu yafi daraja, kai bara in gajarcema idan sana'ar dinki in ta karbi mutum, sai ka ga jama'a na tsoran su ce masa tela, in dan zamani ne sai ka ji sunansa ya zama cif telo in an kwan biyu kuma sai alhaji ko yalla bai.