sana'ar Jima a Kasar Hausa | Majema

sana'ar Jima a Kasar Hausa | Majema

 



Jima babbar sana’ace da  hausawa keyi, duk mai wannan sana’a to gumunsa ya ke ci. Wannan sana’ace wadada ba don yanayin sana‘ar yashafi kazanta amma sana’ace mai tsaftar gaske don badu wani haramci acikin ta sai dai an kauce hanya.

ALSO READ: Asalin Sana'ar sassaka a Kasar Hausa | Masassaka

• Sana'ar Kiwo a Kasar Hausa | Makiyaya

• Sana'ar Fawa a Kasar Hausa | Mahauta

• Takaitaccen Bayani Akan Sana'ar Su | Kamun Kifi

Sana’ar jima har wani dan siddabaru ake mata, na hade-haden jimar. Wanda  bai san yadda ake jema fata ba sai yai zaton da karfin tsiya a ke cire gashin da ke jikin fatar. Amma  da haka bane, siddabarun da a ke mata, shine na hade-haden kayan aikin.

A farko akan sami katuwar kwatanniya a zuba ruwa da Rubin da garin yayan Bagaruwa da kaikayin daddori, idan an yi wannan hadin sai a zuba fatar su kwana biyu su tsumu sannan sai a sami babban dutse ko itace mai fadi wanda zai bada dama a shinfida fatar a jeme, wasu kuma a kan Dutse suke shifidawa wasu kuma a kan turmi su keyi. Idan sun zo yin jimar nan da nan zasu kankare gashin tas kuma a cire duk wata laya da ta ke reto a jikin fatar da kartaji.

Bayan an gama jima an shanya fata, ta bushe, nanma allah yai wa majema baiwa ta canza launin fatar, duk dai yadda a ke son launin fatar akwai yadda a ke mata nata saddabarun irin wannan hadi shi akeyi tun kafin bayyanar turawa ana  sana’ar a kasar hausa.  

Post a Comment

Previous Post Next Post