Sana'ar Fawa a Kasar Hausa | Mahauta

Sana'ar Fawa a Kasar Hausa | Mahauta


 

Sana’ar fawa, sana'a ce da take da tsohon asali, kuma sana’a ce da kowa da kowa zai iya yinta, babu wani haramci ga wannan sana’ar kuma mafi akasarin ma su yin sana’ar a yanzu gadarta suka yi saboda iyayensu da kakanninsu sana’arsu ke nan saboda dadewar sana’ar

Yadda a ke samun ma su karamin karfi a kowace sana’a haka a ke samu acikin mahauta, kuma idan an sami wanda ya ke da nasibi cikin sana’ar sai kaga ya na daga cikin manyan attajiran garin duk girman garin.

Masu wannan sana’a su na  da zabi akan sana’arsu wanda suka rikae dabbobin da ransu suke siyarwa, wasu sukan yanka dabbobin su sai da su a gutsitsire, wa su kuma  agashe, tsire ko kilishi su ke amfani da shi, ma su wannan sana’a su kan taimaka wa kansu kuma su taimakawa
al’ umma don ba kowanne ya iya tsire ba ko kilishi su ke amfani dashi, ma su wannan sana ’a su kan taimaka wa kansu kuma su taimakawa al’umma, don ba kowanne ya iya tsire ba ko kilishi ya na da wani sirri daya akan ajiye shi ya shekara bai yi komai ba.

Mahauta wasu agashe suke siyar da naman. Babban abin sha’awa in ka sami mahauci da yasan sana’ar fawa sosai, sai ka ji yana fadar sunayen ko wace tsoka , ko wani sashe daban-daban da kuma amfaninsu.

A cikin kayan cikin dabba akwai su koda da hanji da timbi da saifa da hanta da zuciya da sauran abin da ba’a rasa ba, haka   kuma yankin nama akwai bashi, da kwanduwa da yadi da takanta da wajiya da tozo da Awaza da namijin nama da farin makari da tantak washi da karfata da saurasu.

Mahauta suna amfani da wukake guda biyu don washi, da gatari don sassara nama ko kashi ko kuma don fidda Tantakwashi, da kuma jan Tadi, ga kuma matsunguri  don hura iska wajen fida. 

Post a Comment

Previous Post Next Post