Mulkin Soja: Mulkin Shugaban Kasa Janar Gowon Da Alkawarin Dawo Da Siyasa A Shekarar 1976

Mulkin Soja: Mulkin Shugaban Kasa Janar Gowon Da Alkawarin Dawo Da Siyasa A Shekarar 1976

 



Janar Gawon ya ci gaba da tafiyar da mulkin wannan kasa ta nigeria inda yayi alkawarin
Dawo da siyasa a shekarar 1976 amma daga baya ya ce wannan lokaci bai dace ba, an samu a gwamnatin tarayya manyan sakatarorin sa sun yi karfi da yawa, kuma suna yin yadda suke so.

ALSO READ: Juyin Mulkin Gwamnatin Buhari a Ranar Talata 27  ga Watan Ogusta 1985 - Asua Daily Post

• Canje  Canjen Mulki a Arewa  Bayan Rasuwar Sardauna

• Mulkin Soja: Kifar Da Gwamnatin Ironsi A Nigeria

• MULKIN SOJA: Hawan Birgediya Murtala Ramat Mohammad Shugaban Kasa

Cin hanci yayi kaka gida, tattalin arziki ya fara ja da baya, abubuwa suka fara tabarbarewa. Haka wasu Gwamnoni suna yin yadda suke so, Na kin yin ayyukan raya kasa da tara dukiyoyin
Jama'a.

Amma a jihar kano sun dace domin zamanin Audu Bako na tsahon shekara takwas (1968-1976), kano ta ga ci gaba da dama kamar
Gina gidan Gwamnatin kano, gina hotel din magwan, Tiga da Daula, Shine ya fara yin tituna masu tagwayen hanyoyi a cikin birnin kano, Ya kuma sa fitilun titin ya gina hanyoyi da yawa, kai mutum ya yi dai dai in yace Gwamna Audu Bako ne uban sabuwar jihar kano.

Post a Comment

Previous Post Next Post