MULKIN SOJA: Hawan Birgediya Murtala Ramat Mohammad Shugaban Kasa

MULKIN SOJA: Hawan Birgediya Murtala Ramat Mohammad Shugaban Kasa

 




A ranar 29 ga watan bakwai na yulin shekarar 1975, janar Gawon ya halarci taron kungiyar hadin kan Africa mai suna OAU inda aka yi masa juyin mulki cikin ruwan sanyi, wanda manyan hafsoahin soja sukayi.

An nada birgediya Murtala Ramat Mohammed a matsayin sabon shugaban kasa, hawan murtala ke da wuya, ya kori dukkan gwamnonin jahohi sha biyu, da dukkan kwamishinonin tarayya, ya yi umarni da a yi tankade da rairaya ga dukkan ma'aikatan kasa.

An kuma shiga shirye - shiryen yadda za'a sake sabon tsarin mulki, dawo da siyasa da ba wa farar hula mulki, Murtala ya kirkiro sabbin jihohi inda ya kara jihohi bakwai suka koma sha tara (19) aka nada sababin Gwamnoni akowace jiha.

ALSO READ: Juyin Mulkin Gwamnatin Buhari a Ranar Talata 27  ga Watan Ogusta 1985 - Asua Daily Post

• Canje  Canjen Mulki a Arewa  Bayan Rasuwar Sardauna

• Mulkin Soja: Kifar Da Gwamnatin Ironsi A Nigeria

A cikin gyare - gyaran da murtala ya kawo har da shirye - shiryen yadda za'a gyara tsarin tafiyar da Kananan hukumomi a cikin shekarar 1975 aka fara tattauna yadda za a yi wa tsarin kananan hukumomi gyaran fuska ta nada wani karamin kwamati domin bin kadin hakan, a farko an bar jihohi su shirya yadda za su tafiyar da kananan hukumominsu, a karshe gwamnatin tarayya ta ga idan ba a yi tsari iri daya ba a kasar za a iya haihuwar dan da bashi da ido.

Gwamnatin tarayya ta yi umarnin kasa kasar shiyya - shiyya don gyara sharin kananan hukumomi domin fitar da ma'anar karamar hukuma, ayyukanta, kudaden batarwa, matsayin sarakuna gargajiya a tsarin aikin rahotanni wadannan shiyya - shiyya an rarraba su a tarurukan da gwamnatin ta shirya shi a ibadan domin yi wa shawarwarin kwaskwarima da duba tsokacin ma'aikatan kananan hukumomi, sarakunan gargajiya da sauran jama'a.

A karshe wadannan shawarwari an gabatar wa da majalissar koli ta soja da majalissar jihohi da suka zauna tare domin zartarwa.
An taron sarakunan kasa a watan bakwai na yulin 1976 domin ba wa sarakuna tabbacin ba karbe musu mulki za a yi ba.

Gwamnatin tarayyar nigeria a watan takwas na Augustan 1976 ta fitar da tsarin tafiyar da kananan hukumomi da ba wa Gwamnoni damar kirkirarsu.

Post a Comment

Previous Post Next Post