Magana Jarice Littafi na Farko | Fara Koyon Mulki Da Baki Kafin Ka Koyi Mulki Da Hannu

Magana Jarice Littafi na Farko | Fara Koyon Mulki Da Baki Kafin Ka Koyi Mulki Da Hannu



Wata rana wadansu aurakai guda biyu suka gane wani itacen baure a bakin wani rafi, kullum suka tashi sai su nufi can su hau su yi ta ci. Gindin bauran kuwa ashe akwai wani kunkuru kullum idan gaurakin nan nacin baure, wadansu yayan su kan fado kasa.

Da kunkuru ya ga  suna fado masa yana ci, sai ya yi tsammani 7 haka da yaga alherin ya yi yawa ran nan sai ya daga kansa ya dubi gauraki ya ce, kai yan uwana nagode!.

Kullum dai nakan ga yayan bauren da ku ke sako mini Abin naku yayi yawa, wallahi har kunyar godiya nake yi Allah dai ya saka da alheri,

ALSO READ: Magana Jarice Littafi na Farko - Munafunci Dodo Yakan Ci Mai Shi

• Magana Jarice: Raina Kama Kaga Gayya Kashi Na Farko 1

• Magana Jarice: Raina Kama Kaga Gayya Kashi Na Biyu 2

Da gauraki suka ji haka, suka duba suka gan shi, sai suka gane abinda ke aukuwa. Har babbar za ta ce masa su ba a kan son su bauren ke zuwa garesu ba sai karamar ta hana ta. Ta dubi kunkuru ta ce Don mun ga kai baka iya hawowa, shi ya sa mu da 77.Allah yaba fiffike mu ke taimakonka. Don dan wannan abu kada ka sa wa kanka wani jin kunya ciki. Allah dai ya bar zumunci.

Kunkuru ya ce Amin! Na ko yi godiya. Suka zauna kan haka. Da abu kamar wasa, har ya zama aminci na gaskiya Gaurakin nan da sun zo da safe, ba abin da suke fara yi sai sun tambayi kwanan kunkuru tukun.suka zauna basa son wani abu ya taba shi shima baya son abin da zai taba su.

Ana nan baya kamar wata guda sai baure ya kare Gauraki suka koma neman kwadi da tana, bayan kamar biyu kuma dan sauran ruwan rafin ya kafe, gurin ya koma kamar ruwa bai taba zama ba. Da gauraki suka ga haka sai suka yi shawarar su tashi su sake wuri, don ba su iya zama sai inda yake da danshi-danshi.

Ran nan har za su wuce sai karamar tace ya kamata muje mu sallami kunkuru, kada ya ga shiru hankalinsa ya tashi, yayi zaton wani abu ne ya same mu, suka tashi suka tafi wajen kunkuru suka gaya masa zasu yi kaura.

Da kunkuru yaji haka sai yace af, ai baku barina sai mu tafi tare Abin da yayi goje ai shi yayi kaura. Ni ina nake iya zama inda babu laima, Da gaurakai  suka ji haka sai suka ce, yaya zaka yi ka bimu Alhali kuwa bakada fiffike.?

Kunkuru yace sai ku dauke ni In kunga kwa iya kokarin hakanan, sai Babbar gaurakar tace wa kake zato cikinmu zai iya daukar kato kamarka, To ce ma muna iya wa ina za'a kama ga ka jiki duk kwarya. Karamar tace barshi muji tasa wata kila yana da wata dabarar kinsan an ce mai rai baya rasa kokari.

Kunkuru yace, Ina da wata yar gurguwar dabara In kwa iya, sai mu sami kara mai karfi kamar zira'i Biyu ni in ciji tsakiyar ku kuma kowacce ta kama gefe guda da baki. Kun ga da haka sai ku tashi da ni har inda zaku. Sai babbar tace wannan dabarar ban ga zata yiwu ba ga kamarka mai surutu
Karamar tace A'a in dai ya iya kyalewa ai sai mu dauke shi.

Ta tashi ta tafi ta samo karan dawa mai karfi ta dauko tazo ta ajiye gaban kunkuru. Ta dube shi tace, To don Allah in kama ban da magana. Kunkuru yace haba wannan ma sai an dankwafe ni kansa sai kace yaro, in yi surutu mana in ina so! Gauraki suka ce To madalla suka kama kara suka tashi da kunkuru yana cije.

Suna cikin tafiya sai hanya tabi dasu ta kasuwa suna kaiwa tsakiyar sai mutane suka daga kai suka hange su, suka ce Eho, eho ku zo ku ga Inda gauraki ke daukar kunkuru kai Jama'a abin mamaki baya karewa nan duniya.

Da kunkuru yaji haka, sai ya fusata yace Kai Allah ya tsine Idanunan nan naku mutane da basa iya ganin abu su kyale, bai gama fadin abin da yake nufi ba sai ya fado kasa kum. Duk da karfin kokon nan nasa ko motsawa baiba ya mutu, gauraki suka wuce abinsu suna bakin ciki suna cewa "Wanda duk bai iya mulki da bakinsa ba lalle yana tare da halaka.

Post a Comment

Previous Post Next Post