Magana Jarice Littafi Na Biyu | In Alllah Ya Taimakeka Kai Kuma Ka Taimaki Na Baya Gareka

Magana Jarice Littafi Na Biyu | In Alllah Ya Taimakeka Kai Kuma Ka Taimaki Na Baya Gareka

 



wani mutum na da alfadari da jaki. wata rana ya tashi za Shi fatauci sai ya sami kaya masu yawa ya labta wa dabbobin nan nasa ya kora ya tafi. suna cikin tafiya har rana ta take ta gota ba su sauka ba. ga hanya ba kyau sai yawan hawa da gangara.ka san jaki karfinsa bai kai na alfadari ba, ashe kuma kayan da aka dara masa sun kwure shi.

Tun yana hakuri, har dai ya gaji ya fara nishi kai, ya dai kare ya bara ya ce wa alfadari, "Don Allah, dan' uwana, ka rage mini kayan nan nawa ka san kai Allah ya yi ka mai kwarin gwiwa ne" Alfadari ya ce "in rage maka akan cin me?" jaki ya ce, A kan girma da arziki, ka ji ko an ce ita ta sa jan sa da abawa"

Alfadari ya ce, "in kana tafiya ka tafi, im ba ka tafiya, shakulatin bangaro angulu ta ga mushen mota." Jaki ya ce, "Don Allah ka taimake ni, ba don halina ba." Alfadari ya ce, "Ahayye, ayyururi, wannan shi ne zancen bara na yi wake bana na yi harawa je ka mace! " Jaki ya ce "wayyo Allah dan' uwana, ka taimaka ni, karfina yakare"

Alfadari ya ce, "wane ne dan'uwan naka ? ni ban gama kame da kai ba. ni dan'uwana doki ne. yaro ko da ganin birni ya san ya fi garinsu." Jaki ya ce, "kada kaza ta yi murna don ta ga ana Jan hanjin 'yar'uwar tata."

Alfadari ya yi shewa, ya ce "yau ga hauka da nade-nade mutuwa ta ga ladani. kai, mai goshi, ba ka sani ba an ce jifa in ta wuce kanka ko kan wa ta fada?"

Da ma karfin jaki ya kare, tafiya dai ya ke yi ba ya ko gani, ga yunwa, ga kaya, ga ubansu duka. yana cikin tafiya ya sa kafa wani rami bai gani ba, sai ga shi rikica kasa, kaya sun danne kan ya nisa ya ce, " A ni tawa ta kare."

Alfadari ya ce "Adankiya fi dam!" farke ya zabura ya kama kayan jaki ya kwance, ya ajiye gefe guda. ya kama wutsiyar jaki ya ciccibe shi, ya ki tashi, sai nishi ya ke yi dai dai

Alfadari ya dube shi, ya ce "wani kaya sai banufa, wace ayagi mai Dan doro. ka tashi, in kana tashi, im bori gaskiya ne ya fada rijiya." Sai farke ya je ya karyo geza, a sami jaki ji ka ke tim-tim-tim, yana cewa "Di, di, di, tashi!" jaki dai tun yana motsi, har ya gaji ya Kai takarda.

Da farke ya ga haka, sai ya cije baki, yana tafa hannu. sai ya koma alfadari, ya kwashe kayan jaki duk ya labta masa. ya dubi mataccen jakinsa kuma Yana cewa, "Turawa sun hana barin mushe a hanya. tsaya in dauki wannan bakina kanin kafata, in kai shi gari, im ba lebura kudi su haka rami su rufe shi, koda likita ya biyo ta nan a ci in tara"

Ya dauki jakin kuma, ya jibga bayan alfadari dai. ya yanki sabuwar geza, ya yi ta ce masa karbi in ya ga yana tafiya sannu sannu. alfadari ya dandana kudarsa, ga kaya ya karu, ga shi tun safe har la'asar sakaliya baici komai ba ga shirga. ya dai Kai gari hasharan majaran, bai san abin da ya ke ciki ba.

Da aka sauke masa kaya, aka ba shi ruwa ya kwankwada, ya kwanta, ya ce "wash, yau an nuna mini gargadi. lalle wanda Allah ya taimaka, shi ko ya ki taimakon na baya gare shi, kome ya same shi ba shi da kaico.

Post a Comment

Previous Post Next Post