Kotu Ta Aika Da Dan Daudun Da Ya Rinka Zabga Ashar Akan Kabari Gidan Gyaran Hali

Kotu Ta Aika Da Dan Daudun Da Ya Rinka Zabga Ashar Akan Kabari Gidan Gyaran Hali

 



Wata kotu a jihar Kano ta aike da Abdullahi Umar, wanda akafi sani da 'Yar Dubu, zuwa gidan ajiya da gyaran hali har zuwa ranar 16 ga watan Satumba mai zuwa domin ci gaba da sauraran karar da aka kai shi.

In baku manta ba ana tuhumar Abdullahi 
'Yar Dubu da kuma wani abokinsa mai suna Mumini wanda tuni ya gudu da laifin hada kai wajen aikata laifin, zage-zage da tayar da tarzoma da kuma laifin tunzura al'umma wanda ya sabawa sashi na 120 da 212 da 341 da 255  da kuma  sashi na 414 cikin baka na kundin penal cord.

A kwanakin baya ne dai aka saki wani bidiyo wanda aka nuna Abdullahi 'yar dubu (Dan Daudu) yana zagi a kan wani kabari a makabarta dake unguwar Mai Dile dake karamar hukumar Kumbotso.

Bayan karanta masa laifinsa yar dubu yace yayi nadama aikata wannan mummunan laifi, Kuma ya kara da cewa yana neman da kotu tayi masa afuwa domin bazai kara aika irin wannan Laifi sharin zuciya ne a cewarsa.

Post a Comment

Previous Post Next Post