A yau ranar juma'a a 5 ga watan Augusta aka wayi gari a Unguwar kofar nassarawa wani yaro dan kimanin shekaru sha hudu ya hau saman gadar kofar nassarawa ( fly over ) inda yasha alwashin bazai sakko ba har sai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka da ga mulki a nata bashi hakuri amma shi sam bai jiba ya dau kimanin awa daya da rabi a makale a wani dan loko dake saman gadar bai sakkoba har sai da jami'an kwana-kwana suka zo,
ALSO READ: Gwamnatin Kano Ta Bayarda Umarnin Ruguje Wani Gini Da Akayi Ba Bisa Ka'ida Ba
• Tarihin Masarautar Kano Daga Mulkin Maguzawa Zuwa Fulani
Zuwan su ke da wuya suka saka masa tsani ( ladder ) idan suku sa masa tsani ta barin da yake sai yakoma wani barin hakadai sai daga baya aka shaho kansa jami'an kwana - kwana suka sakko dashi a inda suka garzaya dashi zuwa ofishin su.
Amma munyi kokarin jin ra'ayoyin mutane inda suke cewa rayuwa ce tai mai kunci wasu kuma suke ce rashin tawakkali ne wasu kuma suna cewa rashin zama a gaban iyaye ne yajan yo masa haka kowa dai da abin da yake fada Allah yasa mudace ameen