Gwamnatin kano karkashin Abdullahi umar Ganduje ta bayarda umarnin ruguje ginin wanda ake tsaka da yinsa a filin kabara, a rana tsaka aka wayi gari rana tsaka ana gini a wannan fili mutane da yawa sunyi tsammanin Gwamnati ce ta siyar da wannan fili kamar yadda ta saba, kwatsam sai Aka wayi gari a ranar litinin 1 ga watan Augusta,
Baffa Babba Dan'agundi ya je da tawagar
Yan Karota yana rushe ginin da aka yi a filin da ke gaban gidan Kadiriyya, sai matasa daga lunguna suka dinga fitowa suna dibar rodikan da aka yi ginin da sunan ganima.
Ginin da mai martaba sarki yace bai san waye mai shi ba, Gwamnan ma yace bai san mai shi ba a cewar Baffa, wani matashin dan gwa - gwarmaya Mai suna Sani Bin Aliyu ya wallafa ra'ayinsa a shafinsa na facebook inda yake cewa,
Ba shakka duk mai hankali zai yarda cewa mai martaba sarki bai san waye mai ginin ba, amma a yanayin da filaye suka tsinci kan su a jahar kano karkashin nagwaggo lafiyaiyyen hankali ba zai yarda cewa nagwaggo bai san da shi ba, In kuwa ta tabbata bai sani ba, to ba wanda ya isa ya sayi wannan filin har ya gina shi ba tare da sanin Gwaggo da kwamishinan kananan hukumomi ba, yakara da cewa kun san ni niba na yin kwai sai da zakara.
Domin kuwa ana tsaka da rushe ginin na tuntubi uku daga cikin yan tsegumi na, wato masu ba ni labari. sun tabbatar min cewa shugaban hukumar hukumar Birni ne ya sayar da filin.
Kuma kafin a rushe sai da Nagwaggo ya biya wanda ya siya kudin filin da kudin duk abin da ya kashe a ginin, kawai an zo cikin dare ne an rushe don jama'a su gani su yi murna kamar yanda kwankwaso ya dinga yi a na sa lokacin, sai ya biya komai, sannan zai rushe duk ginin da yake so don talakawa gidadawa su gani su yi murna.
Misalin haka ta faru a gidan gilas na Zaria Road da kuma filaye da gine ginen da masu hali irin su Baba Aminu Dantata suka yi a filin kofar Na'isa amma idan an ce Nagwaggo bai sani ba, to ai ga gine gine can ana yi har yanzu a cikin masallacin Fagge.
Wadan da har sai da majalisar dokokin jihar
kano ta dakatar da yin su, amma babu abin
da ya tsaya, In kun tuna sun dauka cewa kowa dan Gandujiyya ne ba ya tare da hankalin sa.
Mun wayi gari da labarin cewa wai masallacin Fagge na marigayi sarki Ado ne, kuma an zo da haka ne don kawai a ci gaba da yanka masallacin ana sayarwa, amma mu kaddara Nagwaggo bai sani din ba.
Shin don ALLAH jama'a, makarantu da hanyoyin Amfanin jama'a guda nawa aka yanyanka aka sayar, wadan da kullum kuka mutane suke yi amma abin kullum ci gaba yake yi ba wata hanya a cikin kasuwar sabon gari da ba a yanka an sayar ba, hatta hukumar kashe gobara ta sha yin kokawa a kai, amma kiyau miyau.
Ku kalli abin da ke faruwa a kantin kwari, kasuwar Rimi da dawanau da sauransu, har sun ma hakura sun fauwwalawa Allah, duk ace Nagwaggo bai sani ba, mu ba gidadawa ba ne kar muke kallon kowa amma dai aje ayi ta yi, a cewar sa.