Azumin Tasu'a Da Ashura Tarihin Fara Shi Da Yadda Ake Yinshi Da Falalarshi A Musulunci

Azumin Tasu'a Da Ashura Tarihin Fara Shi Da Yadda Ake Yinshi Da Falalarshi A Musulunci

 



A Musulunci akwai watanni 12, Hudu daga ciki Masu Alfarma ne, kamar yadda yazo a suratul Tauba aya 36, to Almuharram na cikinsu Wadanda aka yi Umurni a Yawaita Azumi a cikinsu, Kari akan haka, Kuma Annabi ya sake yin Umarnin Yawaita Azumin cikinsa har yace, Ba Wani wata da Allah yafi so a Yawaita Azumin cikinshi bayan Ramadan kamar Almuharram.

ASALIN FARA AZUMIN ASHURA

Daga Sayyadatina Aishat R.A, tace Quraishu ta kasance tana Azumin Ashura, lokacin Jahiliyya Kuma Annabi (s a w) ya kasance Yana Azuminsa, Kuma yayi horo da ayi.

CIGABA DA ASHURA A MADINA

Daga Ibn Abbas R.A, Lokacin da Annabi (s a w) ya zo Madina, sai ya samu Yahudawa na Azumin Ashura, yace, Meye haka? Suka ce, Rana ce ta Kwarai, da Allah ya tserar da Musa A.S, da Bani Isra'il daga Makiyin su, sai Annabi (s a w) yace: Nafi Ku cancanta da Musa, sai yayi Azumin yayi horo ayi

MATSAYIN AZUMIN ASHURA

Daga Mu'awiya dan Abu Sufyan R.A, yace: Naji Annabi (s a w) yace: Yau ne Ranar Ashura Amma ba a wajabta maku Azumin ta ba, Amma ni zan yi Azumin, Wanda yaso yayi Azumi Wanda yaso yaci Abinci.

HADA ASHURA DA TASU'A

Daga Abu Musal Ash Ariy R.A yace: Ranar Ashura ta kasance Yahudawa na girmamata suna Rikon ta Ranar IDI, sai Annabi (s a w) yace Amma Ku dai (Kawai) kuyi Azuminta, an karbo daga Ibn Abbas R.A, da Annabi (s a w) yayi Azumin Ashura yayi horo ayi Azumin sai suka ce,  Ya Manzon Allah, Rana ce da Yahudawa da Nasara ke girmamawa sai yace,  idan badi tazo a Riwayar Muslim idan nakai badi insha Allah, zan yi Azumin 9_10 wato TASU'A da ASHURA ( Sai Bai Kai ba S.A.W)

YADDA AKEYI AZUMIN ASHURA

Malamai sunyi bayanin hanyoyi 3, da akeyin Azumin.

1. Ayi Azumin 9, 10 da 11, don ka samu Ladar Azumin Watan baki dayanshi
2. Ayi 9 da 10 (Tasu'a da Ashura) kenan
3. Ko a kalla ayi Ranar Ashura 10 ga watan kenan,

FALALAR AZUMIN TASU'A DA ASHURA.

Azumin ashura yanada matukar falala kuma ana yinsa ne a ranar goma ga watan muharram Annabi (s a w) yana azumtar ranar ashura kuma yayi umarni da ayi kamar yadda yazo cikin wani hadisi.

An karbo daga ibn Abbas (R.T.A) yana cewa, hakika annabi (s a w) yana azumtar ranar ashura kuma yayi umarni da azumtarsa Bukhari da Muslimu ne suka ruwaitoshi Wannan hadisin yana kara tabbatar mana da muhimmancin Azumin ashura.

Shima AZUMIN TASU'A bayaninsa yazo cikin wani hadisi kamar haka, An karbo hadisin daga dan Abbas (R.T.A) yace, Annabi (s a w) ya ce idan rayuwata tayi saura zuwa shekara mai zuwa zanyi Azumin TASU'A, Muslimu ne ya ruwaitoshi, 'Yan uwa idan muka dubi wadannan hadissan guda biyu, zamuga cewa Annabi (s.a.w) ya baiwa Azumin TASU'A da ASHURA muhimmanci sosai.

Post a Comment

Previous Post Next Post