hakkika na yarda da kalamar nan ta hausawa da suke cewa ka san mutum ka san sana'ar sa. domin idan a ka sa mu mutumin daya tsaya ya koyi sassaka ya yi amfani da baiwar da Allah yayi masa sai kaga kamar al'mara, don in wani ya dauki sundukin itace ko wani kwaure wanda mu tsakanin mu da shi sai dai jin dimi ko girki, sai ka ga kafin ka dama fura ka sanye ta har ya ku san mai da shi kudi.
Akwai na zamani masu amfani da inji, amma na da, basu da kayan aiki da yawa, gatari da ake saran itace da shi, sai gizago, da ake gyara sunduki ko, kwauran itace dashi, sai zarto, masassaka na amfani da ita wajen yin zane, idan suna da bukatar yin hakan.
Wata sassakar in an yi a kan gasata da wuta don ya yi kwari ko kuma ya zama ado, kamar akushi. masassaka a yau sune a ke kira kafintoci a yanzu, sune ma su yiwa kujeru irin na da kwaskawarima a canja ma su wani launi,
Ka ga kujera kamar ta aljanu, masassaka har gida su kan gina da katako, mai kyawun gaske, banda manyan abubuwa da suke yi irin su babban bodin mota zuwa su taragun jirgin ruwa.