In kaji ance sa toka sa katsi baba tayi gardama, wannan karin magana ce da hausawa ke yin ta da su ka samu daga cikin sana ar rini, Ada can kafin kan nasara ya waye, ya shiga yawan duniya, har yai ma na wayo Kafin gari ya waye, mu na da marina da su ke rini kaya su canja masu launi, domin ada can mai nisa, kayan da mu ke sakawa farare ne saboda audugar fara ce bata da wata kala,
ALSO READ: Takaitaccen Bayani Akan Sanar Dukanci a Kasar Hausa | Dukawa
• Takaitaccen Bayani Akan Sana'ar Dinkin Hannu Da Dinkin Keke A Kasar Hausa
Don haka marina suke amfani da basirar da Allah yai ma su ta canjawa kaya launi, daga farar kala zuwa shudl ko kuma bakikkirin. don a da ba mu da wa su kalolin da mu ke da su da suka wuce wadannan. Masu sana'ar Rini su kan kebe kan su a wani wuri da ya ke fili su Kan gig gina rijiyoyi masu matsakaicin tsaho wadannan rijiyoyi su a ke kira Baba, watau rijiyar baba kuma matattarar marinan nan ake wa lakabi da katofi.
Rijiyar baba ita marina ke zubawa ruwa da hade-hade kayan aikin Su, toka da garin baba, da katsi su a ke zubawa a cikin wannan rijiya su Juku sai a sayi farin yadi, ko riga sai a tsoma ta a fitar mata da launi da ake sonta, wata kuwa sai a mai da ita gaban Hankaka, har zuwa su rawani ba abursu a baya ba, suma marina na gyarasu harma da kayan mata, musamman aka samu sakakken saki ya turu mace ta daura, sai ka ga ta na canja tafiya a na bude hanci, kamar kasa ba zata dauke ta ba.
A yanzu da yake Zamani ya canja mun dada samun wasu kalolin da bamu da su a da daga wajen turawa akan tura kaya zuwa kala daban-daban kamar su Ja, Kore, Rawaya, amma yadda ake amfani da kayan rini na turawa da namu da banbanci, dan turawa sai dai su hado shi yazo a tisheshshen gari da an zuba sai a tura kayan da ake so,
Turawa suna yi ma na hakane don su kawo rudani cikin lamarin mu, baza su nu na mana ainihin yadda abin yake ba sai dai su kawo shi a hade mu saya amma ba za su nuna mana yadda mu zamu hada ba, Kuma yanzu da yake cigaba yazo, yawancin duk sakar da injina ake yi, tun a wurin sakar turawa kan rina kayan sai dai tufa ta zo a ture amma duk da haka wannan bai sa mun yadda namu hanyoyin rini ba, sai dai rashin kulawa ne yake damun mu daga shugabanni.