Ya tabbata daga Manzon Allah (S.A.W) a cikin hadisin Ummu Adiya (R.A). Wadanda zasu yiwa mamaci wanka su zasu yi la'akari suga wanka nawa ya dace suyi masa, da farko dai kafin a fara wankan da a Kwai abubuwa guda Uku da za'a fara yiwa mamacin Kamar haka,
1. Za'a cire masa suturar da take jikinsa amma za'a sami Dan kyalle a rufe masa al'aurarsa
2. Bayan haka sai Kuma ayi masa tsarki, na bangaren mafuta biyu Bawali da Gayadi
3. Idan mace ce za'a tsefe kitsan da yake kanta, a wanke kan, sannan a Kisha kan guda Uku Sai a kwantar da Kalbar tayi bayan Kan nata
RELATED: Yadda Ake Sallar Gawa a Musulunci
• Yadda Ake Wankan Janaba, Haila, Biki da dai Sauran su
Abu Uku Daga Cikin Sharaddan Wankan Gawa
1. Ana bukatar wadanda zasu wanke mamacin su zamanto makusantan sa, misali, lyaye,ko kanne,ko yayye, ko 'ya'ya da sauransu
2. Ana bukatar maza su jibinci wanke maza, suma mata su jibinci wanke mata (sai dai Miji zai iya wanke matarsa hakama mace zata iya wanke Mijinta
3. Ba sharadi bane lallai sai anyi amfani da ruwan zafi
Ruwa na Farko, Wankan Farko
Wannan wankan za ayi wa mamaci ne wanka irin Wankan Janaba, da farko za'a fara yiwa mamaci alwala ne, kamar irin alwalar sallah, sai dai wajen kuskurar baki da shakar hanci za a Shafa masa ruwa ne kawai a bakin da hancin,
Bayan anyi masa alwala, sai kuma a zuba ruwa a kansa a wanke masa har sau uku, sannan kuma a wanke tsagin jikinsa na dama sannan na hagu.
Ruwa na Biyu Wanka na Biyu
Bayan anyi masa wanka na Sama wato na
Janaba, sai kuma a sami Sabulu ko Magarya ko Kanwa, a wanke mamaci dashi, wato za'a sami Soso da Sabulu a Cuda jikinsa sosai Kamar dai yadda ake wanka irin na Soso da Sabulu, sai dai za'a Iya amfani da Magarya ko Kanwa a maimakon Sabulun, bayan an gama cuda shi sai a dauraye Kumfar da ruwan wankan.
Ruwa na Uku Wanka na Uku
Bayan anyi masa wanka na sama, wato na soso da Sabulu, to sai kuma a sami ruwa na karshe wato na Uku a zuba Turare me Kamshi sosai a ciki, sannan sai a wanke mamaci da shi,
Amfi son ayi amfani da Turaren Kafur, to amma idan ba'a same shi ba to za'a iya amfani da duk wani Turare mai kamshi sosai Bayan an gama wankan Turaren, to sai a tsane jikin mamacin a sa masa Likkafani,
Allah ya mana kyakkyawan Karshe.
Published by: Abubakar D. Bature