A duk lokacin da kazo zaka yi sana'ar kiwon kifi Abu farko da zakayi shine ka tabbata kana da isheshshen Gurin kiwon saboda ba'a son cunkushe kifaye a guri da a duk mita daya (100cm) na gurin kiwon kifi ana iya kiwata kifi 40-50 a tsawon wata 5 zuwa 6.
Ana son mai kiwo ya kara 10% na adadin kifin da zai kiwata. Kamar idan zai kiwata guda 100 to yakar suzama 110 saboda wasu zasu na iya mutuwa.
Yadda Ake Saka Kifi A Cikin Ruwa
Kifi ba sakin danwake ake masa ba a yayin saka shi a cikin ruwa ba, daga gurin da aka sayo shi ana zubo shi a cikin wata roba mai dauke da ruwa. Wanda wannan ruwan ya bambanta da wanda za'a saka kifi.
Ba'a dauko kifi idan rana tayi saidai da safe Ko da yamma, haka kuma idan ya kasance dole lokacin da za a taho dashi rana tayi, to wanda zai taho dashi ya tanaji Kankanra, lokaci bayan lokaci ya dinga taba ruwan, da zaran yaga ya danyi zafi ko kadan ne a canza ruwa ko a sa wannan Kankarar ko kuma a canza ruwa, domin kuwa shi kifi baya son zafi.
Da farko bayan an kawo shi gona Ko gida.
Akan fara canja masa ruwa ne da kashi 25%
za'a kwashe kwatar na ruwan da aka sayo shi da shi sannan a maye gurbinsa dana cikin gurin da za'a saka.
Bayan mintuna 10 sai a sake kwashe 25% a sake maye gurbinsa dana gurin da za'a kiwata kifin, bayan minti 5 sai a sake kwashe rabin ruwan a meye shi dana gurin kiwon, Sannan sai a kifa robar a cikin ruwan gurin kiwon Kifin da kansa zai dinga fita daga robar yana shigewa cikin ruwan da ake so a kiwata shi.