Barkan ku da kasancewa da wannan shafin mai albarka da farko "Asua Daily Post" na kara mika sakon ta'a ziyya a gareku ma'abota kallon wannan shiri na izzarso dama al'ummar musulmi baki daya bisa rashin wannan bawan Allah wanda shine ke Jagorantar wannnan shiri mai farin jini, da fadakarwa, ilmantarwa, dakuma nishadan tarwa, Nura Mustapha waye, Allah ya jaddada rahama a gareshi dan alfarmar shugaba (s.a.w).
In baku mantaba a ranar lahadi wacce tayi
dai - dai da 3 ga watan july 2022 Allah s.w.t
ya karbi rayuwar nura mustapha waye.
Hakika wannan rashi ya girgiza jama'ar masana'antar Kanny wood dama Al'ummar musulmi baki daya Dalili kuwa shine shidai wannan bawan Allah Ya samu kyakykyawar sheda daga mutanen da yake mu'amala da dasu.
A ranar da marigayi nura mustapha waye yarasu Bayan an kai shi makwanci a zan tawar da akayi Da producer na shirin izzar so lawan Ahmad ya bayyana cewa shi dai mariyi nura bashi da abokin fada sannan ko cutar sa zakayi in kahada shi da Annabi s.a.w to zaka cuceshi, sannan kuma bashi da wani aiki fiye da kaunar shugaba (s.a.w)
Dalilin Rasuwar Nura Mustapha Waye
A zantawar da akayi da yar uwar mahaifiyar marigaji nura bayan kammala jana'izarsa, tace Bawani abu da za'a iya cewa shine silar rasuwar Marigayin saboda ko ciwon kai kafin rasuwarsa baice yanayi ba.
Ta kara da cewa a safiyar da nura zai rasu, bayan dawo warsa daga sallar asuba yazo ya gaishe da mahaifiyarsa har ya dauki kudi yabata, Sannan yace taya femasa, sai mahaifiyar tasa tace ai ba abinda kayimin nura sai yace ke dai kiyafe min sai tace nayafema, sannan yakoma Ya kwanta, daga wanna kwanciyar ne Allah s.w.t Ya karbi rayuwar nura, amma bawani abu da za'ace shine sanadiyar Rasuwarsa.