An yi zargin cewar wannan taro na ibadan an shirya kashe dukkan Sarakunan Arewa da suka halarci taron, Sarakunan Gabas da na Yamma an shirya ana cikin taro su fice su bar na Arewa inda bayan sun gama fita za a saka bomb ya kashe dukkan ragowar da ke dakin taron.
Wannan labari ya tonu ga sojoji yan Arewa a karkashin Manjo Murtala Muhammed wanda ya jagoranci juyin mulkin gwamnatin Ironsi a nan ibadan din, suka kama Ironsi zuwa daji suka yi masa abin da ya yi wa Fira Minista sir, ya roke su da neman ba su makudan kudi.
ALSO READ: Juyin Mulkin Gwamnatin Buhari a Ranar Talata 27 ga Watan Ogusta 1985 - Asua Daily Post
• Canje Canjen Mulki a Arewa Bayan Rasuwar Sardauna
• Abubuwan Cigaba Da Gwamna Rimi Yayiwa Kano A Zamaninsa
Ironsi ya furta da bakinsa yana da sa hannu wajen yake kisan Sir. Abubakar Tafawa Balewa, Kasar nigeria ta shiga cikin rudani na kwana biyu 29/7/1966 miladiyya zuwa 31/7/1966 miladiyya, da ta zauna babu shuagaban kasa.
Ranar daya ga watan takwas 1966 shugabannin Juyin mulki suka tabbatar da shugaban sojojin Kasa laftanar kanar Yakubu Gawon, a matsayin Sabon shugaban kasa.