Wata rana wani bakauye wai shi kado ya dauki gatarinsa, ya shiga daji zai yiwo itace, Dajin nan kuwa da yam fashi, mutanen da ke kauyen nan kuwa duk sun san dasu. can bakauyen nan yayi nisa cikin daji, sai ya hango wani abu zube yana daukar ido, ya matsa ya ga ko mene ne, sai ya taradda sulalla ne a zube birjik.
Ya waiwaya baya, ya waiwaya gaba bai ga kowaba, sai yaduka ya cika aljihun taguwarsa fal, Ya saba gatarinsa ya sheka da gudu ya nufi gida.
Ya rabu da wajen da ya debi kudin nan ke nan, sai ya gamu da yam fashi su uku, suka ce masa, kai tsaya! me ya koro ka?, Kado ya tirje a tsora ce yana tsammani kudin nan da ya debo nasu ne Sai yace "Iye Ni? Na'am mutuwa nagani a fili shi ya sa na ke gudu.
Yam fashin nan suka yi dariya, suka ce ”Mutuwar da kanta ka gani, ko kuwa maciji dai?" Kado yace ni wallahi mutuwar ce da kanta na gani a can zube, shi yasa ban ko tsaya wurin ba, don kada a ce na gan ta, na sheko da gudu.
RELATED: Magana Jarice: Raina Kama Kaga Gayya Kashi Na Farko 1
• Magana Jarice: Raina Kama Kaga Gayya Kashi Na Biyu 2
Da yam fashin suka ga lalle ya tsorata da su sai suka ce, masa "To muje ka kai mu muganta mu ma, " kado ya wuce gaba suna biye, har wajen da kudin nan suke, yace ga ta! Na rantse da Allah kuwa ban diba ba, kada kuce na diba ne. Yana boye - boyen aljihu yana tsammani ajiyarsu ce, shi ya sa ya kara rudewa haka.
Da Allah yasa basu duba Aljihunsa ba sai suka ce, To tafi, in ka fadi kuwa muna zuwa da dare mu yanka ka. Koda kado ya ji haka sai ya ranta cikin na na kare, bai zame ko ina ba sai gida, ya kai yana haki Kamar ransa zai fita, ya boye kudinsa,
Ya kama bakinsa ya shuke.
Da yam fashin nan suka ga ya wuce, sai suka yi mamakin kudin nan suka ce "Watakila wadansu barayi ne suka sato da suka ga sun yi musu yawa Suka zubad da sashi nan, Allah sarki! Bakauyen nan fa tsammani yake kudin nan namu ne, Babbansu yace ai ko ya firgita yanzu ya dade da kaiwa gida.
Sauran suka ce haba tuni da ya fita a gujen nan ai ko mota ba ta kamo shi. Suka bushe da dariya, Sai babban ya dauki sule guda ya ba karamin, ya ce ruga kasuwa ka sayo mana abinci muci tukun, idanummu su bude sa'an nan mu san yadda zamu yadda zamuyi kasafin wannan Karamin ya karba ya sa riga kamar ba barawo ba, Yayi nadi ya tafi kasuwa ya nufi wajen mai tuwo ya sayo, ya kuma biya mahauta ya sayo musu tsire ya dora kan tuwon, ya dauko ya nufo daji yana kulle kellen abin da zai aikata da kudin nan da nasa ne shi kadai, sai yaga itacen dinya ya ajiye kayansu, yace Alhamdulillah!
Bari in debi ruwan dinya in zuba wa abincin nan, in kai musu, nikuwa ko sun ce in ci, sai na ce na ciyo daga kasuwa, ka ga d sun ci duk sai su mace, ni kuma in kwashe karfena, in shiga gari in yi ta kece raini, ya karya dinya ya zuba. Shikuma ashe kafin ya dawo yan uwansa sun yi shawara da ya zo su kashe shi, su kwace kudin su raba su kadai suka ce ai haka abin ya fi auki.
Can sai wannan karamin ya iso da kayan abinci koda ajewarsa sai suka hau masa da bugu, bai san hawa ba bai san sauka ba suka kashe shi, Suka fara cin abinci in sun gama su kwashe kudi su san inda suka nufa, dagama cinye abinci, sai kowanne ya fara kaduwa yana faduwa yana tashi, Kafin kiftawa da bismilla duk suka kai takarda.
Can bayan kamar kwana bakwai sai kado yace a ransa bari in koma wurin wurin nan, in na tarar suna kwashe kudinsu in tsuguna in yi kala, ko Allah ya ba ni dan taro, in kuwa na tarad da su sai in ce na zo ne in gaya musu sarki zai aiko da dogarai a kama su gobe, abin da yafi kowa yayi ta kansa, In ce kuma abin da yasa na gaya musu, don sunji kai na ne ran nan, kaga watakila ma sa bani dan sule kudin dai gasu zube kamar ba su so, ba alamar karewa.
Da isar sa wurin sai ya tarad da su duk sun mutu, yayi juyayin abin da ya kashe su ya rasa, da ya lura har kuraye sun ci su, sai yayi zaton sune suka kashe su, ya rasa abin da zai yi don murna ya shimfida gwadonsa ya kwasa yayi yan kirare ya dora, don kada a gane ya kai gida, ya haka rami ya binne, magariba na yi kuma ya kira dansa suka tafi suka kwashe saura, ya zauna ya yi tacin kudin sa sannu a hankali dashi da dansa ba wanda ya gane.
Godiya
ReplyDelete