Juyin Mulkin Gwamnatin Buhari a Ranar Talata 27 ga Watan Ogusta 1985 - Asua Daily Post

Juyin Mulkin Gwamnatin Buhari a Ranar Talata 27 ga Watan Ogusta 1985 - Asua Daily Post

 



Gwamnatin Buhari ta wayi gari an kifar da ita a wani juyin mulkin cikin gida a ranar talata 27 ga ogustan shekarar 1985 miladiyya, masu juyin mulkin sun sanar da dalilian su na yin juyin mulki ta bakin wani hafsan soja mai suna Birgediya Joshuwa Nimiyal Dogon Yaro.

A cikin dalilan sun hada da rashin daukar shawarwarin sauran shugabannin sojo, da yin mulkin kama karya da babban hafsa a fadar shugaban kasa Manjo Janar Babatunde Idiagbon yake yi.

A karshe dai an sanar da samun sabon shugaba inda aka nada Shugaban Sojan Kasa Manjo Janar  Ibrahim Badamasi Babangida, da yake wannan juyin mulki na cikin gida ne canje canjen da aka samu bashi da yawa a jihar kano, an dauke gwamnan kano Hamza Abdullahi an nada shi Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja.

An nada Kwamandan Birget na Sojan kasa dake Abeakuta Kanar Ahmad Muhammad Daku mukamin sabon gwamnan kano na soja, hawan wannan gwamna ke da wuya ya yi gyara a majalisar Kwamishinoni.

Gwamna Daku ya nada kwamishinoni kamar haka, Abubakar S. Kura sakataren gwamnati, Ibrahim Isma'il kwamishinan yada labarai, Adamu Shehu Hadeja kwamishinan masana 'antu da ciniki, Usman Sambo kwamishinan ayyuka da gidaje, Abba Abdullkahi kwamishinan kudi, Rabi Ilyasu kwamishiniyar jin dadi da walwala, Muhammadu Kazaure kwamishinan Lafiya, Sunusi Chiroma Yusuf kwamishinan Shari'a, Musa Shu'aib kwamishin kananan hukumomi, Muhammadu Kazaure kwamishinan Gona,

A zamanin gwamnan kano Daku aka shirya yin gidauniyar Jihar Kano, An tara miliyoyin nairori domin yin ayyukan raya kasa, Madaki Bello na cikin manyan yan kwamitin masu shirya wannan gidauniya, kusan tun lokacin da aka mayar da taron zuwa kananan hukumomi, inda duk sarki bai je ba shi ne yake wakiltarsa.

A watan satumban 1986 miladiya, sabon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi canje - canjen Gwamnoni inda ya dauke gwamnan kano Ahmad Daku zuwa Sokoto, Aka dauko Gwamnan Jihar Kwara Wing Commander Ndatu Umaru zuwa Kano.

A wannan zamani na Ndatu Umaru aka assasa noman alkama a kano, ya kawo abubuwan ci gaba masu yawa da zaman lafiya a masarautar kano.


Post a Comment

Previous Post Next Post